'Ba Su da Amana," Gwamnan Zamfara Ya Fadi Matsayarsa kan Sulhu da 'Yan Bindiga

'Ba Su da Amana," Gwamnan Zamfara Ya Fadi Matsayarsa kan Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da ’yan ta'addar da ke kashe mutanensa ba
  • Dauda Lawal ya tabbatar da hakan lokacin da ya kai ziyarar jajantawa garuruwan Kagara, Dan Isa, da Kasuwar Daji da aka farmaka
  • Gwamnan ya kuma yi alkawarin gyara hanyoyin kauyukan uku da ya ziyarta domin inganta zirga-zirga da rayuwar mutanen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake nanata matsayarsa kan sulhu da 'yan ta'addar da ke kashe mutanen Zamfara ba dare ba rana.

Gwamna Dauda Lawal ya fadawa mutanen Zamfara cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da 'yan bindiga ba, kuma za ta doge kan hakan.

Gwamnan Zamfara ya sha alwashin kin yin sulhu da 'yan bindiga
Hoton Gwamna Dauda Lawal a lokacin da ya kai ziyara garuruwa 3 na Zamfara. Hoto: @s_balaIdris
Source: Twitter

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana matsayar gwamnan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar Zamfara ya ziyarci garuruwa 3

Sulaiman Idris ya ce Gwamna Dauda ya jaddada matsayarsa kan sulhun ne a ranar Alhamis lokacin da ya ziyarci wasu garuruwa da 'yan bindiga suka farmaka.

A cewar mai magana da yawun gwamnan Zamfara, garuruwan da Dauda Lawal ya ziyarta sun hada da Kagara, Dan Isa da kuma Kasuwar Daji.

Dukkanin wadannan garuruwan suna karkashin karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara, kamar yadda Legit Hausa ta fahimta.

Sanarwar Sulaiman ta yi nuni da cewa gwamnan ya ziyarci garuruwan ne domin jajanta masu tare da fada masu kokarin gwamnati kan samar a tsaro a jihar.

'Babu sulhu da 'yan bindiga' - Gwamnan Zamfara

Gwamnan Zamfara ya jaddada wa mutanen garuruwan da ya ziyarta cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da miyagun ba, cewar sanarwar.

"A jiya, na fara kai ziyarar jajantawa ga wasu daga cikin garuruwan da 'yan bindiga suka farmaka a kwanakin nan. Tun da ba mu iya kammala wa ba jiya, shi ne na ci gaba da ziyarar a yau.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

"Mun ziyarci garuruwa uku, inda na hadu da mutanensu tare da jajanta masu kan abin da ya same su, na kuma yi masu magana cikin karfafawa gwiwa.
"Tun lokacin da na hau mulki, na fito fili na fadi matsaya ta, ba zan taba yin sulhu da wadandan 'yan ta'addar da ke kashe mutanemu ba, kuma ina nan kan bakata."

- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.

Gwamnan Zamfara ya yi alkawarin gayara titunan garuruwa uku da ziyarta
Tagawar Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal a ziyarar da ya kai garuruwa uku na Kaura Namoda. Hoto: @s_balaIdris
Source: Twitter

Gwamnan Zamfara zai gyara hanyoyin kauyuka

Gwamna Dauda Lawal ya ci gaba da cewa:

"Tsaro shi ne farko a fannonin da gwamnatina ta mayar da hankali a kansu, kuma mun sadaukar da komai domin ganin mun samar da tsaro.
"Burina shi ne na ga mun kare rayuka da dukiyoyin mutane na. Don haka ne ma gwamnatina ba za ta taba yin sulhu da 'yan bindiga ba, saboda ba su da amana ko kadan."

Gwamnan ya ce a lokacin da yake shiga kauyukan, ya fahimci titunansu sun lalace don haka ya yi alkawarin gyara masu domin su ma su samu saukin zirga-zirga.

Karanta sanarwar a kasa:

Addu'ar gwamna ga masu hannu a ta'addanci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Dauda Lawal ya nuna damuwa kan ci gaba da kai hare-hare da yan bindiga ke yi a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gaji da hare hare, ya roki Allah game da masu daukar nauyin ta'addanci

Gwamnan Zamfara ya roƙi Allah ya tona asirin masu daukar nauyin hare-haren, ya kuma wulakanta su, yana mai kira ga jama’a da su dage da addu’a.

Ya sha alwashin ci gaba da daukar matakan gaggawa domin kare dakile hare-haren yan bindiga wanda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyin al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com

iiq_pixel