Gwamnan Zamfara Ya Bude Kofar Sulhu da 'Yan Ta'adda
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ce za a iya yin sulhu da 'yan ta'adda bisa wasu sharuda da ya gindaya kafin amince wa da hakan
- Dauda Lawal ya ce an sha yin sulhu da 'yan ta'adda, amma ba sa mutunta yarjejeniyoyi, wanda ya sa gwamnatinsa ke yaki da su
- Ya ce duk da ya bayyana sharudan yin sulhu da 'yan bindigar, wannan ba ya nufin gwamnatinsa ta shirya shiga yarjejeniya da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai yiwuwar yin sulhu da ƴan ta'adda bisa sharadin da zai amfani jama'ar da ya ke jagoranta.
Sharudan da gwamna Dauda Lawal ya bayar sun hada da cewa dole sai 'yan ta'addan sun daina kashe mutane, sannan sai sun zubar da makamansu baki daya.

Kara karanta wannan
Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji

Asali: Facebook
A wata hira da ta kebanta da BBC Hausa, Gwamna Dauda ya ce raguwar sharadin shi ne su mika wuya ga hukumomi, wanda zai tabbatar da cewa sun bar kisan bayin Allah da gaske
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Zamfara na shirin sulhu da 'yan ta'adda?
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa kalamansa ba sa nufin an shirya yin sulhu da 'yan ta'addan da su ka addabi jiharsa.
Sai dai ya na ganin idan har za a yi sulhun, dole ne a yi gaskiya da kuma adalci ga wadanda aka kashe, da sauran wanda 'yan ta'addan su ka illata a baya.
Gwamnan ya ce:
"Akwai da yawa wadanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu, wasu matansu. Saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, ba wai kullum a riƙa fifita ƴan bindiga ba."
Zamfara: Ana nasara a kan 'yan ta'adda
Da yake karin bayani kan irin nasarorin da jami’an tsaro ke samu a jihar, Gwamna Dauda ya ce an kashe sama da 'yan ta’adda 50 a ranar Juma’a a garin Tingar Fulani, kusa da Zurmi da Shinkafi.

Kara karanta wannan
"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki
Gwamnan ya kara da cewa an kashe manyan shugabannin mugayen mutanen da ke tare da fitaccen dan ta’adda Bello Turji, wanda ake farautarsa ruwa a jallo a halin yanzu.
'Yan ta'addan da aka kashe a Zamfara
Daga cikin wadanda Dauda Lawal ya ce an yi nasarar kashe wa akwai Sani Mainasara, Sani Black, Kachallah Auta, Audu Gajere. Kabiru Jangero, Dangajere da makamantansu
"Wannan nasara da ake samu za a ci gaba da samunta har sai mun kawo ƙarshen lamarin. Ko dai su ajiye makamansu, ko kuma ba za mu bar su ba," a cewar gwamnan
Dalilin gwamnan Zamfara na kin sulhu
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ya na shakku a kan maganar sulhu da 'yan ta'adda ne ganin yadda ba sa iya mutunta yarjejeniyar da ake da su.
Ya ce:.
"An yi sulhun nan ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma abin da ake so."
Matsayar gwamnatoci a kan sulhu da 'yan ta'adda
A wani labari, kun ji cewa an fara samun masu ra'ayin a yi sulhu da 'yan ta'adda domin kawo karshen asarar rayukan daruruwan bayin Allah da ake fama da shi a jihohi daban-daban.
Yayin da gwamnatocin Zamfara da Katsina ke ganin bai dace a rika yin sulhu da miyagun mutanen ba, gwamnan Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa sulhu zai iya zama alheri ga jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng