Tirkashi: Gwamatin Tinubu Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 3.6 a Gyaran Gada 1 Kacal

Tirkashi: Gwamatin Tinubu Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 3.6 a Gyaran Gada 1 Kacal

  • Gwamnatin tarayya ta ce gyaran gadar Third Mainland zai ci Naira tiriliyan 3.8, yayin da ginin gadar zai ci Naira tiriliyan 3.6
  • Gwamnati ta ce babbar gadar ta lalace ne sakamakon tono yashi da ake yi ba bisa ka’ida ba, zaizayar ƙasa, da lalacewar ƙarfe
  • A taron majalisar FEC, an amince a gaggauta gyaran wasu gadoji a Najeriya, ciki har da gadar Jalingo, Keffi, Mokwa da Jebba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnati za ta gyara ginin gadar Third Mainland da ke Legas a kan Naira tiriliyan 3.6.

Ya ce barin gadar a mummunan yanayin da take ciki yanzu zai zama babban kuskure, domin gadar ce tafi kowacce samun zirga-zirga a kasar.

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kashe kimanin Naira tiriliyan 3.6 domin gyara gadar Third Mainland da ke Legas
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Gwamnati za ta gyara gadar Legas kan N3.6trn

Kara karanta wannan

Saudiyya, Amurka da wasu kasashe za su shigo Najeriya, za a dauki matasa aiki

Ministan ayyukan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a Abuja, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

David Umahi ya ce binciken baya-bayan nan ya gano ginshikai da wasu muhimman sassan gadar sun lalace, ta yadda za su iya durkushewa a kowanne lokaci.

A cewarsa, abubuwan da suka jawo lalacewar gadar sun hada da tono yashi da ake yi a kasan gadar ba bisa ka’ida ba, zaizayar ƙasa da kuma lalacewar ƙarfe saboda tsatsa.

Ministan ya bayyana cewa an kiyasta kudin aikin gyaran zai kai Naira tiriliyan 3.8, yayin da gina sabuwar gada gaba ɗaya zai iya cin kimanin Naira tiriliyan 3.6, wanda ya fi sauki kaɗan.

Gwamnati za ta fita neman kudin ayyukan

David Umahi ya sanar da cewa:

“Mun samu amincewar gwamnati na amfani da aƙalla manyan kamfanoni bakwai domin su gudanar da cikakken bincike, ƙirƙirar tsari, da gabatar da tayin farashi a karkashin tsarin EPC+F."

Ministan ya kara da cewa sakamakon binciken ya yi dai-dai da rahoton baya kan gadar Carter da ke a Legas, inda kamfanin Julius Berger ya ce ba za a iya gyaranta ba, tare da bada shawarar rushe ta da gina ta gaba ɗaya, wanda hakan zai iya lakume Naira biliyan 359.

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

A cewar Umahi, FEC ta amince da neman hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) don aikin, tare da fara tattaunawar nemo rancen kuɗi daga manyan masu bayar da aro na duniya, ciki har da bankin Deutsche.

“Ba za mu iya jinkirta aikin nan ba. Ko a gyara ko sake gina ta, za a kashe makudan kudi a aiki musamman saboda za a yi amfani da injiniyoyi mafi ƙwarewa."

- David Umahi.

Ministan ayyuka, David Umahi ya ce gwamnati ta amince a gyara wasu gadoji a sassan Najeriya
Ministan ayyuka, David Marka yana duba aikin gina tituna da ake yi a wasu sassan Najeriya. Hoto: @realdaveumahi
Source: Twitter

Za a gyara gadoji a sassan Najeriya

The Guardian ta rahoto ministan yana cewa FEC ta amince a gaggauta gyara wasu gadoji da suka lalace a fadin ƙasa, ciki har da gada gadar Jalingo a Taraba da gadar Ido (wacce gobara ta lalata).

Sauran gadojin sun hada da gadar Keffi a Nasarawa, gadar Mokwa a Neja, gadar hanyar Abuja zuwa Kogi, gadojin kan hanyar Legas zuwa Ibadan, gadar Jebba a Kwara, da gadar hanyar Itokin zuwa Ikorodu a Legas.

“Za a rubuta bayanan aikin dukkanin gadojin domin a tura su cikin gaggawa ga shugaban ƙasa ta hannun ma’aikatar kuɗi domin amincewarsa."

- Ministan ayyuka, David Umahi.

Gwamnati za ta gina tashoshin bas 6

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da kashe N142.02bn don gina tashoshin bas na zamani a shiyyoyin jihohi shida.

Yayin da majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta ba kamfanin Planet Project kwangilar aikin, an ce za a gina tashoshin a jihohin Abeokuta, Gombe da su Kano.

Ministan sufuri, Sa'idu Alkali bayan kammala taron FEC ya ce aikin zai karfafa tsaro, kara jin dadin fasinjoji, tare da kuma bunkasa kasuwanci a shiyyoyin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com