Wata motar BRT ta kama da wuta a gadar third mainland

Wata motar BRT ta kama da wuta a gadar third mainland

Daya daga cikin motocin da ake amfani da su wajen zirga-zirgan jama’a a Lagas wacce aka fi sani da BRT ta kama da wuta a gadar third mainland.

Motar wacce ta doshi hanyar Iyana-Oworo ta kama da wuta ne bayan ta wuce yankin Adeniji Adele akan gadar.

Annobar da ya afku a gadar, wanda shine mafi tsawo daga ciki gadaje uku da suka hada birnin Lagas zuwa cikin gari ya haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar.

Ma’aikatan hukumar kashe gobara na jihar Lagas da na LASTMA na wajen inda suke kokarin kashe wutar da kuma daidaita cunkoson da aka samu.

Babu bayani akan rasa rai a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki 18 zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cew Hukumar Kula da Gidajen Yari (NPS) na babban birnin tarayya, Abuja ta kama wani Clement Jacob da laifin yunkurin safarar wani ganye da ake kyautata zaton wiwi ne zuwa cikin gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Kakakin hukumar, Chukwuedo Humphrey sanar da cewa wanda ke ake zargin mazaunin kauyen Deidei a Abuja ya boye ganyen wiwin ne a cikin takalminsa da ya ke shirin mikawa wani fursuna, Emeka Onyejikacki da ake tsare da shi saboda samun shi da muggan kwayoyi.

Humprey ya ce asirin wanda ake zargin ya tonu ne yayin da aka lura ya yi canjin takalmi da fursunan da ya zo ganawa da shi a lokacin da zai tafi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel