Sheikh Kabiru Gombe Ya Samu Sarauta, An Ga Manyan Malamai na Taya Shi Murna a Hotuna
- An nada sakataren kungiyar Izala na Najeriya, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe a sarautar Modibbon Lau a jihar Taraba
- Fitaccen malamin addinin musuluncin ya karbi takardar wannan nadin sarauta daga hakimin Lau, Alhaji Abdullahi Ibrahim na Chindo
- Malam Kabir Gombe na daya daga cikin malaman sunnah da suka yi fice wajen karantarwa musamman a mimbarin kungiyar Izala
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Muhammadu Kabiru Haruna Gombe ya samu sarauta a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
An nada Sheikh Kabiru Gombe, sakataren kungiyar Jama'atu' Izalatil Bidi'a Wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS) a sarautar Modibbon Lau.

Source: Facebook
Kungiyar JIBWIS ta Najeriya wacce aka fi sani da Izala ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa tare da hotuna a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nada Sheikh Kabiru Gombe a sarauta
Sanarwar ta ce hakimin Lau da ke karamar hukumar Lau a jihar Taraba, Alhaji Abdullahi Ibrahim na Chindo ya amince da nadin Malam Kabiru a matsayin Modibbon Lau.
A hotunan da kungiyar Izala ta wallafa, an ga Sheikh Kabir Gombe dauke da takardar nadin sarautar da aka masa a hukumance.
Hotunan sun kuma nuna yadda manyan malaman kungiyar Izala suka taya Kabiru Gombe murnar samun wannan sarauta.
Malaman Izala sun taya Kabiru Gombe murna
Daga cikin wadanda aka gani suna taya malamin murna akwai shugaban kungiyar Izala na Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Sauran sun hada da shugaban Izala na jihar Kano kuma shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da wasu malamai da alarammomi.
Kungiyar Izala ta fitar da sanarwa
Sanarwar ta ce:
"Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya zama sabon Modibbon Lau.
"Mai girma hakimin Lau, Alh Abdullahi Ibrahim na chindo, ya naɗa babban sakataren kungiyar JIBWIS, Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, a matsayin ‘Modibbon Lau’.
"A madadin ƙungiyar Izala, muna taya shi murna tare da addu’an Allah ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa. Amin."

Source: Facebook
Takaitaccen bayani kan Sheikh Kabiru Gombe
Sheikh Kabiru Gombe dai yana daya daga cikin malaman Izala da suka shahara a Najeriya, nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
Malamin ya fito daga jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya kuma ya zama sakataren Izala na kasa tun daga watan Disamba, 2011 zuwa yau.
Mutane da dama sun taya Sheikh Kabiru Gombe murnar wannan nadi tare fatan Allah Ya sa hakan ya kara masa kwarin gwiwar ci gaba da karantarwa.
Sheikh Bashir Aliyu ya zama shugaban SCSN
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) ta sanar da naɗin Sheikh (Dr.) Bashir Aliyu Umar, a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa.
Hakan dai na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, wanda aka bayyana a matsayin rashi ga al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Fitaccen malamin musulunci daga Kano, Dr. Bashir sananne ne a fagen ilimin addinin islama da kuma tsarin harkokin kuɗi a Musulunci a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

