Jerin Manyan Kujerun Gwamnatin Tarayya da Tinubu Ya ba Mutanen Kano a Shekaru 2
Duk da yadda wasu yan siyasa a Arewa ke kuka da wariya a rabon manyan muƙamai a gwamnatin tarayya, za a iya cewa jihar Kano ta samu rabo a tafiyar da gwamnatin Bola Tinubu.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tun bayan kafuwar gwamnatin ne Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya riƙa rabon muƙamai a matakai daban-daban ga wadanda ke mara masa baya daga Kano.

Source: Facebook
Legit ta tattara wasu daga cikin manyan kujerun da Tinubu ya raba ga ƴan APC da su ka fito daga jihar Kano.
Sun haɗa da:
1. Ganduje ya rabauta a gwamnatin Tinubu
Jaridar Punch ta ruwaito tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin waɗanda su ke cin moriyar muƙami a gwamnatin Tinubu.
Bayan zama Shugaban Jam’iyyar APC tun daga 3 ga Agusta, 2023, kafin ya yi murabus, Tinubu ya nada Ganduje a matsayin Shugaban Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) a Janairu 2025.
Sai dai a doka, jam'iyya ce ke da hurumin zaben shugaba, watakila da albarkacin shugaban kasa.

Source: Twitter
Wannan mukami zai ba shi damar da ido a kan harkokin zirga-zirgar jiragen sama, da kuma jagorantar ayyukan filayen jirage a Najeriya.
2. Tinubu ya ba Dr. Mariya Bunkure muƙami
Gwamnatin Bola Tinubu ta nada Dr. Mariya Mahmoud Bunkure a matsayin Karamar Ministar Abuja a watan Agusta, 2023.
Tana aiki tare da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike kan tsare-tsaren kara sabunta Abuja, da kara raya birnin.
Dr. Mariya na daga cikin jajirtattun 'yan gwamnatin Kano a zamanin Abdullahi Umar Gnaduje, kuma ta samu mukamin ne bayan Tinubu ya janye sunan Maryam Shetty daga jerin wadanda za a bai wa mukami a wancan lokaci.
3. Yadda Gwarzo ya samu Minista na shekara 1
Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya rike mukamin Karamin Ministan Gidaje da raya karkara a gwamnatin daga watan Agusta, 2023 zuwa Oktoba 2024.
Ya taka rawar gani a wajen shirye-shiryen samar da gidaje a karkashin shirin “Renewed Hope”.
Ya bar mukamin ne a lokacin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa a shekarar 2024.
4. Ata ya maye gurbin Gwarzo a FEC
Yusuf Abdullahi Ata ya karbi muƙamin Gwarzo a watan Oktoba 2024, inda ya ɗora a kan manufofin Bola Tinubu na samar da gidaje a wasu jihohi, daga ciki har da Kano..
Ata, Tsohon Kakakin Majalisar Dokoki ta Kano ne, inda kwarewarsa a siyasa ke taimakawa wajen hada kai tsakanin gwamnati ta tarayya da ta jihohi a harkar gidaje.

Source: Original
Haka kuma makusanci ne ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin.
5. Tinubu ya naɗa Pakistan Shugaban NAHCON
Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Abdullahi Usman Saleh Pakistan watan Oktoba 2024 a matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).
A yanzu haka, shi ne ke jagorantar kula da jin dadin mahajjata, daidaita farashin aikin hajji, da tabbatar da bin ka’idoji ga hukumomin hajji na jihohin kasar nan da sauransu.
6. Ja'oji ya samu muƙami a gwamnati
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta naɗa Nasir Bala Aminu Ja’o’ji babban Mashawarcin Shugaban Kasa kan Jama’a da Jagoranci.
An nada shi a watan Agusta 2025, inda aikinsa ya hada da wayar da kan jama’a, da horas da shugabanni a fadin kasar nan.
Dan siyasa ne daga Kano wanda ya shahara wajen hada matasa da shirye-shiryen wayar da kai da motsa jam'iyya.
7. Abdulaziz ya zama hadimin Tinubu
AbdulAziz AbdulAziz, shi ma ya shiga jerin Hadimai Tinubu inda aka naɗa shi Mashawarcin Shugaban Ƙasa a kan jaridu.
An nada shi a 2023, kuma gogaggen dan jarida ne da ke kula da dabarun yaɗa labarai ta jaridun da ake bugawa daga fadar shugaban kasa.
8. Ramat ya shiga gwamnatin tarayya
Gwamnati ta nada Abdullahi Garba Ramat a watan Agusta 2025 a matsayin shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya.
Zai mayar da hankali inda masu amfani da wutar lantarki da kuma jawo masu zuba jari a fannin domin inganta shi.

Source: Facebook
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ungogo ne a Kano a lokacin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
9. Shugaban kasa ya naɗa Dr. Mustapha a muƙami
Gwamnatin Tinubu ta nada Dr. Abdullahi Mustapha a watan Oktoba 2023, inda yake jagorantar tsare-tsaren makamashi na kasa, bincike, da bai wa gwamnati shawara kan makamashi.
A wani sako da gwamnatin ta wallafa, ta bayyana shi a matsayin ƙwararre a fannin aikin injiniya, mai hangen nesa na amfani da bayanai da fasaha wajen bunkasa makamashi.
10. An naɗa Ma’aji Shugaban NWDC
Shugaban kasa ya nada Shehu Abdullahi Ma'aji a matsayin shugaba na farko na hukumar, Ci gaban Arewa maso Yamma.
Ma’aji zai riƙa kula da ayyukan cigaban noma, da tattalin arziki a yankin Arewa-Maso-Yamma da zummar ƙara farfaɗo da su.
Ɗan asalin ƙaramar hukumar birnin Kano ne, kuma yana da kwarewa a ilimin fasaha da aikin gwamnati.
11. Tinubu ya naɗa ɗan Kano muƙami a NASENI

Kara karanta wannan
Kungiyoyin Arewa sama da 1,000 sun tsaida wanda za su zaɓa tsakanin Tinubu da Atiku a 2027
An nada Khalil Suleiman Halilu a Satumba 2023, inda yake jagorantar cibiyar bunkasa kirkire-kirkire ta Najeriya ta NESANI.
Matashi dan kasuwa ne daga Kano, mai sha’awar kera motoci masu amfani da wutar lantarki da bunkasa masana’antu.
12. Kano: Tinubu ya yi wa soja muƙami
An nada Air Marshal Hassan Bala Abubakar, babban Hafsan Sojan Sama a 19 ga Yuni, 2023, don jagorantar rundunar sojin sama ta Najeriya.
Ɗan asalin ƙaramar hukumar Shanono ne kuma gogaggen soja ne mai shekaru da dama a aiki da ke mayar da hankali kan fatattakar ƴan ta'adda a ƙasar.
13. Ɗan Kano ya samu muƙami a PenCom
Bola Ahmed ya naɗa Hafiz Ibrahim Kawu a matsayin Kwamishina a Hukumar PenCom a watan Agusta 2025, inda yake taimakawa wajen kula da harkar fansho.
Tsohon dan majalisa ne daga Tarauni, kuma yana daga cikin ƴan Kano da su ka samu muƙamai a gwamnati kamar yadda Hon. Yusuf Gagdi ya tabbatar a Facebook.
14. Tinubu ya ba Gawuna kujera a FMBN

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye
Gwamnati ta nada Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a watan Janairu 2025, inda yake jagorantar hukumar bayar da lamunin gidaje ta tarayya.

Source: Facebook
Tsohon Mataimakin Gwamna ne a Kano, kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2023 kuma an fara ba shi kujera ne a majalisar jami'ar BUK.
15. 'Ya 'yan Ganduje sun samu muƙamai
Asiya Umar Ganduje tana wakiltar Kano a hukumar cigaban Arewa-Maso-Yamma, inda take tabbatar da bukatun jihar suna shiga cikin shirye-shiryen yankin.
A gefe guda kuma an ji labarin yadda 'danuwanta Umar Abdullahi Ganduje ya samu matsayin Babban Darekta a hukumar REA a karkashin gwamnati mai-ci.
Sauran waɗanda su ka samu muƙami
16. Hamza Ibrahim Baba
Wasu daga cikin waɗanda su ka samu muƙaman Tinubu daga jihar Kano sun haɗa da Hamza Ibrahim Baba, Manaja a shirin bayar da rancen gwamnati na GEEP.
Daily Nigerian ta wallafa cewa an nada shi a Mayu 2025, inda yake jagorantar shirin bayar da kananan rance ga ‘yan kasuwa da kananan masana’antu.
17. Janar Abdulmalik Jibril
Sai Janar Mai Ritaya Abdulmalik Jibril da aka naɗa Sakataren Hukumar CDCFIB da ke kula da daukar ma’aikata da ladabtar da jami’an ɗamara .
18. Ismaeel Ahmed
Sai Ismaeel Ahmed da aka naɗa a ranar 27 ga Yuni, 2025, inda yake jagorantar shirin mayar da man mota zuwa gas mai tsabta (CNG) a Najeriya.
Lauyan tsohon shugaban matasan APC ne kuma tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, da ke da kwarewa a shari’a da manufofin gwamnati.
19. Abdullahi Tanko Yakasai
Abdullahi Tanko Yakasai hadimi ne ga shugaban kasa, yana taimakawa Mai girma Boa Tinubu wajen hulda da jama'a a Arewa maso yamma, kamar yadda ta wallafa a shafinta.
20. Ummusalma Isiyaka Rabiu
Shugaba Bola Tinubu ya nada Louis Odion da Ummusalma Isiyaka Rabiu a matsayin kwamishinonin FCCPC, inda majalisar dattawa za ta tabbatar da su.
Sauran mutanen Kano da ke rike da ofis a yau sun hada da Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai wanda aka nada shugaban sabuwar jami'at kiwon lafiya ta Tsafe.
Bayan masu aiki da gwamnatin tarayya a bangaren zartarwa, akwai 'yan siyasar Kano da-dama da ke rike da mukamai a majalisar wakilai da ta dattawa.
Fatima ta ƙi muƙamin Tinubu
A baya, mun wallafa cewa a watan Yuni 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Dakas Dakas a matsayin shugaban Hukumar NLRC.
Haka kuma ya tabbatar da naɗin Uchenna Okolocha da Fatima Alkali a matsayin kwamishinoni a hukumar da ke wakiltar sashen da su ka fito a Najeriya. Sai dai a lokacin gabatar da rahoton tantancewa, shugaban kwamitin shari’a na majalisar dattawa, ta samu labarin cewa Fatima Alkali daga Arewa maso Gabas, ta ƙi karɓar mukamin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng





