Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Sarkin Musulmi Ya Yiwa Tinubu, Gwamnoni da 'Yan Najeriya
- Sarkin Musulmi ya yiwa shugaban kasa, gwamnoni, da duka shugabanni da mabiya nasiha kan halin kuncin da ake ciki a yau a Najeriya
- Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci shugabanni su rika tsayawa suna sauraron koken talakawa da kunnen basira don magance su
- Ya ce halin da ake ciki a kasar nan jarabawa ce daga Allah, yana mai cewa idan mutane suka dogara da Shi zai kawo sauki a rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya kara jan hankalin shugabanni kan sauraron koken talakawan Najeriya.
Sultan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu, da duka gwamnonin jihohi 36, da sauran shugabannin siyasa a ƙasar nan da su saurari ƙorafin ’yan Najeriya.

Asali: Facebook
Sarkin ya ce maimakon ku rika dode kunnenku idan mutane sun koka kan halin da ake ciki, ya dace a nuna musu tausayawa tare da kwantar musu da hankali, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Da gaske ba shi da lafiya? Gwamna ya fadi halin da ya tarar da Shugaba Tinubu a Aso Rock
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Muhammadu Sa'ad III, wanda ya yi wannan magana ne a taron ƙaddamar da littafin tarihin NASFAT domin tunawa da cikar ƙungiyar shekara 30, rahoton Punch.
Nasihar da Sarkin Musulmi ya yi
Sultan ya nuna damuwarsa kan ƙarancin ilimi a tsakanin matasan ƙasar, tare da yin kira ga ’yan Najeriya da su rika yi wa shugabanni addu’a maimakon zaginsu.
“Ina kira ga shugabanninmu su kalle mu da idon tausayi irin na uba ga ɗa. Duk wata matsala da kuke da ita, duk wani kuka da kuke ji, kada ku kori mutane.
"Adalci shi ne tubalin kowace al’umma. Kamar yadda Sheikh Abdulrauf ya ce, ƙasa na iya tsira tare da rashin imani, amma ba za ta tsira da rashin adalci ba. Don haka mu fuskanci adalci a duk abin da muke yi.
"Shugabanninmu da mabiya, duk muna buƙatar zama masu adalci a duk ayyukanmu. Mu faɗa wa kanmu gaskiya a duk abin da muke yi da yadda muke yi.
"Mu yi imani cewa Allah ya kawo mu duniya domin mu bauta masa. Don haka mu cigaba da yin aikin alheri, mu bar sauran ga Allah, musulmi da waɗanda ba musulmi ba, mu rika yi wa shugabanninmu addu’a a kowane lokaci.”
- In ji Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Asali: Twitter
Menene mafitar wahalar da ake sha a Najeriya?
Basaraken ya bukaci yan Najeriya su dauki halin da ake ciki a matsayin jarabawa daga Allah, kuma su yi kokarin cin wannan jarabawa ta hanyar jajircewa.
"Ina da yakini 100% cewa Allah zai kawo sauƙi gare mu gaba ɗaya a wannan ƙasa. Mu koma gare shi shi kaɗai, domin shi kaɗai ne mai bayarwa, shi kaɗai ne mai ɗauka," in ji shi.
Sarkin Musulmi ya kawowa gwamnatin Tinubu mafita
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Musulmin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kammala aikin madatsar ruwa ta Kashimbila da ke jihar Taraba.
Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa aikin na da matuƙar tasiri wajen warware matsalolin wutar lantarki da ke addabar Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Laraba a wajen taro kan zuba hannun jari a Taraba wanda aka gudanar a Jalingo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng