Ba Daraja: Ƴan Sanda Sun Cafke Basarake kan Zargin Aukawa Ƙaramar Yarinya
- Rundunar ‘yan sandan Gombe ta kama wani Dagaci bisa zargin aukawa wata yarinya ‘yar shekara 12 da haihuwa
- Kwamishinan ‘yan sanda Bello Yahaya ya yaba wa jami’an da suka damke barayin kayan lantarki, karafan jirgin kasa
- Rundunar ta gargadi jama’a su rika kai rahoton duk wani abin da ake zargi cikin gaggawa, tana mai jaddada kudirin kare rayuka da dukiyar jama’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi bajinta bayan cafke wasu mutane da dama kan laifuffuka daban-daban.
Rundunar ta sanar da gano kayan lantarki da aka lalata, bututun ƙarfe, da karfuna na layin dogo a Bajoga, tare da kama wani dagaci bisa zargin fyade.

Source: UGC
Nasarorin da yan sanda suka samu a Gombe
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi Dam Roni shi ya bayyana nasarorin da aka samu a fadin jihar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta kuma kama wani shahararren dan fashi da makami da aka dade ana nema tare da wiwi, da wasu mutum bakwai bisa zargin hadin baki da sata.
An gano kayan da aka lalata a Bajoga bayan samun kiran gaggawa daga tashar motar kamfanin simiti na Ashaka, inda wadanda ake zargi suka tsere kafin zuwan ‘yan sanda.
Bincike ya nuna bututun na mallakar kamfanin Ashaka ne, yayin da wayoyin lantarki da kusoshi ake zargin an kwace su ne a kan hanyar Bajoga–Jalingo.
Basarake ya shiga hannu kan cin zarafin yarinya
Haka kuma a ranar 9 ga watan Agustan 2025, rundunar a yankin Zambuk ta samu rahoton cewa Mohammed Tukur, mai shekara 55, ya yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade.
‘Yan sanda sun kai ta asibitin Zambuk domin binciken likita, sannan suka kama wanda ake zargi, bincike yana ci gaba kan lamarin.
Rundunar ta yi Allah-wadai da duk nau’in cin zarafin mata, ta kuma bukaci jama’a su rika kai rahoto cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
'Yan sanda: "Yan siyasa a kano sun yi alkawarin hana zubar da jini a zaben cike gurbi"

Source: Original
Gombe: An cafke barayin karafan layin dogo
A ranar 11 ga watan Agustan 2025, rundunar yan sanda a Gona ta kama mutum uku da karafan jirgin kasa guda 19 a cikin mota Toyota.
Sun amsa cewa sun cire kayan ne daga layin dogo a Nassarawo, bincike ya kuma kai ga kama karin mutum hudu ciki har da masu karɓar kayan sata.
An dauki hotunan kayan sannan aka mika su ga sashen bincike na SCID domin ci gaba da shari’a.
Kwamishinan ‘yan sanda ya yaba da saurin martanin jami’an, yana jaddada kudirin kare rayuka, dukiya, da kayayyakin gwamnati a jihar Gombe.
An kama limami kan cin zarafin yarinya
Mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sanda a Osun ta kama wani malamin addini da ake zargi da lalata wata yarinya ‘yar shekara takwas a Ede.
Lamarin ya faru a unguwar Babasanya-Araka inda jama’a suka taru suka kai hari kan wanda ake zargin kafin a mika shi ga jami'an Amotekun.
Jami'in Amotekun da wasu mazauna sun tabbatar da cewa wanda ake zargin limami ne kuma yana koyar da Alkur’ani a unguwar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
