'Yan Najeriya Sun Rage Sayen Fetur, NMDPRA Ta Lissafa Jihohi 4 da Aka Fi Shan Mai

'Yan Najeriya Sun Rage Sayen Fetur, NMDPRA Ta Lissafa Jihohi 4 da Aka Fi Shan Mai

  • Hukumar NMDPRA ta ce sayan man fetur ya ragu a watan Yunin 2025 zuwa lita biliyan 1.44, idan aka kwatanta da watan Mayu
  • Duk da cewa an dan samu karin kaso 1.73 na rarraba man dizal da kananzir, amma an ce an raga amfani da fetur sosai a Yunin 2025
  • NMDPRA ta ce Legas ce a kan gaba a jihohin da aka fi rarraba wa man fetur da lita miliyan 205.66, sai Ogun da lita miliyan 88.69

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa 'yan Najeriya sun rage sayan mai a watan Yuni 2025, inda aka sayar da iya lita biliyan 1.44.

Daraktan sashen hulda da jama’a na hukumar NMDPRA, George Ene-Ita, ya tabbatar da hakan cikin wani rahoto da ya fitar a ranar Laraba, 13 ga Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 3 ana farautarsa, babban dillalin kwayoyi a Najeriya ya shiga hannu

An rahoto cea 'yan Najeriya sun rage sayen man fetur a watan Yunin 2025
'Yan Najeriya na sayen fetur a gidan man NNPCL domin zirga-zirga da wasu bukatu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton sayar da dizal da kananzir a Yuni

George Ene-Ita ya ce an saba ganin 'yan kasar na sayen akalla lita miliyan 48 kullum, amma adadin ya ragu zuwa lita miliyan 38.94 a Yuni, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in ya kara da cewa:

“Jimillar man da aka sayar a watan Yunin 2025 ya kai lita 1,440,768,129, wanda ya nuna raguwar kaso 16.42 idan aka kwatanta da lita 1,768,812,804 da aka sayar a Mayun 2025, raguwar da ta kai sama da lita miliyan 290.”

Rahoton NMDPRA ya nuna cewa a watan Yunin 2025, an samu karin kaso 1.73 na man dizal (AGO) da aka sayar, inda aka sayar da lita miliyan 432.18 idan aka kwatanta da lita miliyan 424.83 da aka sayar a Mayun 2025.

An samu raguwar sayen fetur a Yunin 2025

Sai dai kuma, adadin man dizal (TO) da aka fitar da shi zuwa kasuwa ya ragu da kaso 23.23, daga lita miliyan 552.35 a watan Mayun 2025 zuwa lita miliyan 424.06 a watan Yunin shekarar.

Kara karanta wannan

Abin farin ciki: Hauhawan farashin kaya ya sauka a Najeriya, an bayyana dalilin saukin

Haka nan, an samu raguwar fitar da man kananzir da sayar da shi da kaso 13, inda aka iya sayar da lita miliyan 7.79 kawai a watan Yunin 2025, ƙasa da kusan lita miliyan tara na watan Mayun shekarar.

An samu babban koma baya a bangaren sayar da man fetur, wanda rahoton ya nuna ya ragu da kaso kusan 48, daga lita miliyan 72.36 a watan Mayun 2025 zuwa lita miliyan 37.66 a watan Yunin shekarar.

Baya ga raguwar masu sayen man fetur din, hukumar NMDPRA ta ce an ma samu raguwar rarraba fetur din zuwa gidajen sayar da mai da kaso 16.54 a Yunin 2025.

Hukumar NMDPRA ta ce za ta zage damtse wajen tabbatar da rarraba mai a fadin kasar nan
Jami'an hukumar NMDPRA suna rufe wasu gidajen man fetur da aka same su suna algus. Hoto: @NMDPRA_Official
Source: UGC

Jihohin da aka fi kai wa man fetur

Rahoton NMDPRA ya kuma fayyace adadin lita biliyan 1.44 na man fetur da aka fitar a watan Yunin 2025 zuwa jihohi daban-daban, inda Legas ta samu mafi yawa.

An ce Legas ta samu lita miliyan 205.66, sai Ogun da ta samu lita miliyan 88.69, yayin da babban birnin tarayya ya samu lita miliyan 77.51 da kuma Oyo da ta samu lita miliyan 72.81.

Rahoton ya nuna cewa:

“Raguwar rarraba man ya na nuna irin kalubale da ake ci gaba da fuskanta a masana'antar man, wanda ya shafi masu amfani da mai a ƙasar kai tsaye."

Kara karanta wannan

Mummunan hadari a Kano ya jawo asarar rayuka sama da 10

Duk da haka, NMDPRA ta sha alwashin yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa rarrabawa da tabbatar da isar da man ba tare da yankewa ba a fadin ƙasar.

'Mun koma hawa acaba ko tafiyar kasa' - Yunusa

Malam Yunusa Lanbar Rimi, ya shaidawa Legit Hausa cewa shi yanzu ya daina hawa motarsa, ya koma hawa acaba, adaidaita sahu ko kuma ya yi tafiya a kasa.

"Allah ina fada maka Sani, ni na kwana biyu bana hawa mota ta. Kuma da yake babu nisa sosai tsakanin gidana da shagona, to ba na wani damuwa da ita, sai na hawa acaba na tafi kasuwa.
"Idan ka ga na yi amfani da mota, to doguwar tafiya ne, ko wani abu na gaggawa da ba za mu iya jiran abin hawa ba, saboda wahalar ta yi yawa malam.
"Da kudin makarantar yara zan ji, ko da kudin haya, ko kudin cefane da dawainiyar yau da kullum, ai abin da yawa. Ita kuma mota kullum sai dai ka ba ta, ita ba ta baka."

- Yunusa Lanbar Rimi.

Auwalu Bala, daga garin Faskarin jihar Katsina, ya ce har yanzu yana hawa mashin dinsa, amma dai ya rage zirga zirga.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

"Mu tun da aka shiga wannan sauyin rayuwar muka daina yawo. Idan ba na gida ina kasuwa, idan na tashi daga kasuwa ina gida, ziyarar 'yan uwa ce kawai ke fitar da ni jefi-jefi."

Auwalu Bala, wanda ke sana'ar sayar da nama da noma ya koka kan yadda hare-haren 'yan bindiga a Faskari ya hana su noma tsawon shekaru.

Ya ce:

"Shekaran jiyar nan sojoji suka rika yanke dawa da masarar mutane, wai barazana ne ga tsaro a inda aka girke su. Wannan masifa har ina, ace noman da ka samu ka yi ma, an zo an sare shi.
"Dama mu mun shekara biyu cur ba mu yi noma ba, har na rani da ina yi, amma yanzu bana yi, kowa na tsoron zuwa gona ya hadu da mutanen nan na."

Dangote ya rage farashin litar man fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masu sayen man fetur a gidajen mai na iya samun sauki yayin da matatar matatar Dangote ta rage farashin kowace lita.

Matatar hamshakin attajirin ta sanar da yin ragin N30 kan kowace litar man fetur da take sayarwa ga 'yan kasuwa masu dillancin man kai tsaye daga wajenta.

Hakazalika matatar Dangote ta bayyana cewaza ta fara amfani da manyan motoci masu aiki da iskar gas (CNG) da ta sayo don rabon fetur a fadin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com