Wata Sabuwar Masifa: Ƴan Sanda Sun Kama Matuƙin Babur Ɗauke da Ƙoƙon Kan Mutane 3
- Rundunar ‘yan sanda ta kama Kadir Owolabi da Jamiu Yisa kan zargin mallakar kokon kan mutane uku a yankin Ijebu na jihar Ogun
- Mai magana da yawun rundunar, Omolola Odutola, ta ce binciken farko ya kai ga kama Yisa bayan an kama Owolabi dauke da kokunan
- An ruwaito cewa ba wannan ne karon farko da jami'an 'yan sanda suka kama mutane dauke da kokon kan mutane a jihar Ogun ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun – Rundunar ‘yan sandan Ogun ta fara tuhumar wasu mutane biyu, Kadir Owolabi da Jamiu Yisa, bayan an kama su da kokon kan mutane uku a yankin Ijebu na jihar.
'Yan sanda sun fara kama Owolabi ne a ranar Litinin yayin da yake kan babur a hanyar Ijebu Ode/Ibadan dauke da kokon kan mutane.

Asali: Twitter
An kama matashi dauke da kokon kan mutane
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ta sanar da hakan a ranar Talata kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
“A ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025, da misalin karfe 2:00 na rana, tawagar 'yan sanda daga 71 PMF Awa Ijebu suka fara gudanar da binciken tsaro na yau da kullum.
"Wannan binciken ya faru ne a babbar hanyar Ijebu Ode/Ibadan, kusa da sha-tale-talen sansanin 'yan gudun da ke Oru Ijebu.
“Yayin da suke bincikar ababen hawa, jami’an 'yan sandan sun tsayar da wani Kadir Owolabi wanda ke kan babur. Binciken da aka yi a jakarsa ya sa an gano abin kokon kan mutane uku."
Ogun: 'Yan sanda za su zurfafa bincike
Omolola ta kara da cewa binciken farko ya kai ga kama wani Yisa mai shekaru 53 a bayan karamar hukumar Ijebu Ode.
“Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun kama maza biyu da ake zargi da mallakar kokon kan mutane uku a yankin Ijebu na jihar Ogun,” in ji ta.
Kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Ogunlowo, ya umurci sashen binciken manyan laifuffuka na jihar da su ja ragamar binciken don kawo karshen cikin sauri.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun na nanata kudirinta na daukar matakin gaggawa kan aikata duk wani nau'in laifi, yayin da take neman hadin kan jama’a a ayyukanta."

Asali: Original
Kamen masu dauke da kokon mutane a Ogun
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da ake kama mutane dauke da kokon kan mutum a jihar Ogun ba.
A watan Janairun 2025, askarawan Ogun sun kama wani Adelani Oriyomi mai shekaru 54 a makabartar Kere, Obada-Oko, Abeokuta yana kokarin tono kokon kan mutum.
Haka kuma a watan Oktobar 2023, Oyenekan Oluwaseyi, wani faston cocin Christ Liberty Evangelism da ke Rosco, Iyana Iyesi, Ota ya shiga hanun 'yan sanda.
An kama Oyenekan Oluwaseyi tare da wasu mutum uku a unguwar Saje, Abeokuta bayan an same su dauke da kokon kan mutum, kamar yadda muka ruwaito.
An kama mutumin da ya cire kokon kai 50
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an kama wani mutumin da ke shiga makabarta yana sace kokon kan mamatan da aka birne, sai ya yi tsafi da su.
An sha jin labarin yadda ake sace kokon kan mamata a yankin da lamarin ya faru a jihar Ogun, lamarin da ya sa shugabanni suka fara daukar mataki.
Ya zuwa yanzu, rundunar 'yan sanda na ci gaba da bincike don gano bakin zaren lamarin kafin daga bisa a gurfanar da mutumin a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng