Fursunoni Sun Farmaki Jami'an NCoS, Sun Tsere daga Gidan Yarin Keffi

Fursunoni Sun Farmaki Jami'an NCoS, Sun Tsere daga Gidan Yarin Keffi

  • Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi bayan sun farmaki jami’an tsaro, inda suka ji wa biyu munanan raunuka
  • Hukumar NCoS ta ce an cafko bakwai daga cikin 16 da suka tsere yayin da ake ci gaba da farautar sauran fursunonin da suka gudu
  • Shugaban NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci gidan yarin, inda ya ce za a hukunta duk jami'in da aka samu da laifi a lamarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali da ke Keffi, jihar Nasarawa, da safiyar Talata bayan sun lalata tsarin tsaron wurin.

Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, Umar Abubakar, ya ce sai da fursunonin suka yi galaba kan jami’an da ke bakin aiki sannan suka tsere.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi da ke jihar Nasarawa
Shugaban hukumar NCoS yana tuba bayanai bayan fursunoni sun tsere a gidan yarin Neja. Hoto: @CorrectionsNg
Source: Twitter

Sanarwar Umar Abubakar ta ce jami’ai biyar ne suka jikkata a harin, inda biyu ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali, a cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fursunoni 16 sun tsere a jihar Nasarawa

Sai dai fursunoni bakwai daga cikin wadanda suka tsere ba su yi dogon zango ba aka sake kamo su, yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda sauran tara suka buya.

Hukumar kula da gidajen gyaran halin ta yi wa jama'a karin bayani kan abin da ya faru, tana mai cewa:

“Wasu daga cikin fursunoni sun farmaki jami'an tsaron da ke bakin aiki tare da jikkata su, wana ya ba fursunoni 16 damar tserewa daga gidan gyaran halin.
“Jami’ai biyar sun samu raunuka daban-daban, inda biyu daga cikinsu ke kwance a asibitin da ke cikin gidan yarin cikin mawuyacin hali.
“An samu nasarar sake cafke fursunoni bakwai daga cikin wadanda suka tsere, kuma yanzu suna hannun hukuma."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai hari 'Gidansu Atiku,' sun yi garkuwa da mata

Shugaban NCoS ya yi kakkausan martani

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa shugaban hukumar NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin bayan faruwar lamarin, inda ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan dalilan da suka jawo aka yi fashin magarkamar.

A yayin ziyarar, Sylvester Nwakuche ya ce za a dauki mataki mai muni ga duk wani jami’in hukumar da aka samu da hannu a tserewar fursunonin, inji rahoton The Guardian.

Haka kuma ya umurci a hada rundunar hadin gwiwa tsakanin jami'an NCoS da sauran hukumomin tsaro domin fita farautar fursunonin da suka tsere.

Hukumar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kuma kasance a ankare don kai rahoton duk wani motsi ko wani mutum da ba su yarda da shi ba.

Hukumar kula da gidajen yari za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro don kamo fursunonin da suka tsere a Keffi
Shugabannin hukumar kula da gidajen yari (NCoS) suna rangadi a gidan yarin Neja da aka fasa. Hoto: @CorrectionsNg
Source: Twitter

Hukumar NCoS za ta nemi taimako

Sanarwar Umar Abubakar ta ci gaba da cewa:

“Sylvester Nwakuche, ya ziyarci cibiyar, ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan yadda suka tsere. Ya ce ba za a kyale duk wani jami’i da aka samu da laifi ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

“Bugu da kari, ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da sauran hukumomin tsaro domin kama wadanda suka tsere.
“Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilan tserewar, hukumar na tabbatar da jajircewarta wajen ba da tsaro a gidajen gyaran hali na fadin kasar nan."

Fursunoni 7 sun tsere a Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa fursunoni bakwai sun tsere daga gidan yarin Ilesa da je jihar Osun, ana tsakiyar sheka ruwan sama.

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ce ta hada kai da sauran jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin kamo fursunonin da suka tsere.

Wannan ba shi ne karo na farko da hakan ke faruwa ba, domin a 2024 an samu irin wannan tserewa a Maiduguri bayan madatsar ruwa ta fashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com