Bayan Jiran Wata da Watanni, Gwamna Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70000

Bayan Jiran Wata da Watanni, Gwamna Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70000

  • Gwamnan Cross River, Bassey Otu ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000 bisa yarjejeniya da ƙungiyar ƙwadago
  • Gwamnatin jihar ta tabbatar da aiwatar da sabon albashi ga ma'aikatan ne a matsayin martani ga masu nuna yatsa ga gwamna
  • Hakazalika, gwamnatin Otu ta bayyana shirinta na mayar da ɗaruruwan ma’aikatan wucin gadi zuwa cikakkun ma’aikatan jiha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Cross River - Gwamna Bassey Otu ya tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar Cross River.

Shugaban ma’aikatan Cross River, Dakta Innocent Eteng ya ce Gwamna Otu ya cika alkawarin da ya daukar wa ma'aikatan jihar.

Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Otu ya fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000
Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Otu yana rattaba hannu kan wasu muhimman takardu. Hoto: @officialspbo
Asali: Twitter

Gwamnan Cross River ya fara biyan sabon albashi

Dakta Innocent Eteng ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Talata a Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta jika makoshin ma'aikata, an fara biyansu hakkokinsu bayan jinkurin watanni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake magana jim kaɗan bayan kaddamar da shirin tarukan bikin Ranar Ma’aikatan Gwamnati, Eteng ya bayyana cewa gwamnatin Otu ta aiwatar da mafi ƙarancin albashin kamar yadda aka rubuta a yarjejeniyar.

Dakta Eteng ya ce:

“Mai girma gwamna ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, kuma mun aiwatar da shi kamar yadda aka rubuta a yarjejeniyar.
“Wadanda suke cewa gwamna bai aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba jahilai ne kuma marasa fahimtar yadda shugabanci yake.
"A matsayina na shugaban ma’aikata, ina magana da cikakken iko. Wannan bayanin da nake baku, tabbatacce ne, kuna iya zuwa bakuna ku tabbatar."

Gwamna Otu ya cikawa 'yan kwadago alkawari

Dakta Eteng ya tabbatar da cewa gwamnatin Otu ta aiwatar da mafi ƙarancin albashi na ƙasa bayan kammala yarjejeniyar da ƙungiyar ƙwadago.

“Ina gaya muku cewa an aiwatar da mafi ƙarancin albashi a duk faɗin jihar, a dukkan matakai, ba tare da saba wa ka'idojin yarjejeniya ba. Ya kamata ku yaba wa gwamna kan wannan aiki."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'

- Dakta Innocent Eteng.

Shugaban ma’aikatan ya bayyana wasu daga cikin shirye-shiryen bikin Ranar Ma’aikatan Gwamnati, da suka hada da tattakin da ma’aikata za su yi a cikin gari.

Sauran sun hada da taron wayar da kan jama'a, bayar da lambar yabo ga kwararrun ma’aikata, jawabi na musamman daga sakataren gwamnatin jihar, da sauransu.

Gwamna Bassey Otu ya ce zai daga darajar ma'aikatan wucin gadi zuwa cikakkun ma'aikatan gwamnati
Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu zai mayar da ma'aikatan wucin gadi zuwa cikakkun ma'aikata. Hoto: @officialspbo
Asali: Facebook

Gwamna zai daga darajar wasu ma'aikata

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Bassey Otu ke shirin mayar da ɗaruruwan ma’aikatan wucin gadi da ke aiki a ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassan gwamnati daban-daban (MDAs) zuwa cikakkun ma'aikatan jihar.

Dakta Eteng ya bayyana hakan a jiya yayin jawabi ga ƙungiyar manyan sakatarori da daraktoci, a matsayin wani ɓangare na tarukan bikin makon ma’aikatan gwamnati na bana.

Rahoton da Legit Hausa ta gani a shafin gwamnatin Cross Rivers ya nuna cewa fiye da kashi ɗaya bisa huɗu na ma’aikatan gwamnati 20,000 da jihar ke da su ma’aikatan wucin gadi ne.

Kara karanta wannan

'Najeriya ka iya wargajewa kafin zaɓen 2027': Tsohon minista ya yi hasashe

Rahoton ya kuma nuna cewa da dama daga cikin ma'aikatan wucin gadin sun shafe shekaru suna aiki alhalin ana biyan su tsakanin N5,000 zuwa N10,000 a wata.

Gwamna Bassey Otu zai goyi bayan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Bassey Otu ya ba Shugaba Bola Tinubu tabbacin cewa zai samu kashi 96 na kuri'un jihar Cross River a 2027.

Otu ya ce Tinubu ya cancanci tazarce la'akari da cewa gwamnatinsa ta bunkasa tattalin arziki da rushe sansanonin ‘yan ta'adda da masu tayar da kayar baya.

Ya ce bikin 'Carnival' na bana zai ja hankalin duniya, sannan shirin noma na jihar ya dace da tsare-tsaren kasa gaba daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com