FG Tana Gayyatar Kwararrun Ma'aikatan Gwamnati Da Su Nemi Gurbin Akanta Janar

FG Tana Gayyatar Kwararrun Ma'aikatan Gwamnati Da Su Nemi Gurbin Akanta Janar

  • Gwamnatin tarayya tana gayyatar kwararrun ma'aikata gwamnati da su nemi gurbin akanta janar na tarayyar Najeriya
  • A sanarwa da Yemi-Esan ta fitar, Shugaba Buhari ne ya amince da a nada sabon akanta janar kuma kwararre wanda ya kai matsayin darakta
  • Kamar yadda takardar tace, ma'aikatan gwamnati da suka kai mataki na 17 kuma ba zasu yi ritaya ba ha zuwa watan Disamban 2024

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bukaci kwararrun ma'aikatan gwamnati da su nemi kujerar akanta janar.

Wannan cigaban na zuwa ne bayan Idris Ahmed, tsohon akanta janar na tarayya ya shiga hannun EFCC kan zargin sama da fadi da N80 biliyan.

Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya
FG Tana Gayyatar Kwararrun Ma'aikatan Gwamnati Da Su Nemi Gurbin Akanta Janar. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ministan kudi, Zainab Ahmed, ta dakatar da Idris har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Kara karanta wannan

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

TheCable ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da Nada Anamekwe Nwabuoku ya jagoranci lamurran ofishin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da aka fitar ranar 21 ga watan Yunin 2022, Folasade Yemi-Esan, shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, tace an fara kokarin nada sabon akanta janar.

Kamar yadda Yemi-Esan tace, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince kan cewa wadanda suka ga sun cancanta da su nemi kujerar.

TheCable ta ruwaito cewa, kujerar a bude take ga daraktoci da akantoci wadanda ke aiki da tarayya kuma ba za su yi ritaya ba har zuwa karshen shekarar 2024.

"Bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ofishin shugaban ma'aikatan tarayya yana gayyatar masu son maye gurbin akanta janar na tarayya da su miko bukatarsu," takardar tace.
"A saboda haka, dukkan akantoci na sama a gwamnatin tarayya wadanda suka kai matsayin daraktoci da albashi mataki na 17 zuwa ranar ko kafin 1 ga watan Janairun 2020 kuma ba zasu yi ritaya ba kafin ranar 31 ga watan Disamban 2024, duk za su iya neman gurbin.

Kara karanta wannan

Direban Tasi da ya Mayar da N438k da Aka Manta a Motarsa ya Samu Babban Aiki, Ya Bayyana Hotuna

"Duk wani jami'in dake fuskantar ladabtarwa ba zai iya neman kujerar ba."

Takardar ta umarci wadanda suka dace da su mika takardunsu inda ta kara da cewa ranar ko kafin 6 ga watan Yulun 2022 za a rufe.

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A wani labari na daban, bincike kan makuden kudaden da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, game da dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, ya haura ya kai N170 biliyan, rahoton jaridar The Nation ya bayyana.

Idris, wanda a daren jiya ya ke neman a bada belinsa, ya bayyana sunayen wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu cikin handamar kudaden kasar da ake tuhumarsa a kai.

Hukumar EFCC ta tuhumi wani babban sakataren gwamnati kan wasu daga cikin kudaden da ake zarginsa da rub da ciki a kai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030

Asali: Legit.ng

Online view pixel