Mutuwa Ta Shiga Filin Kwallo, Mataimakin Koci Ya Mutu ana Tsakiyar Atisaye a Ogun

Mutuwa Ta Shiga Filin Kwallo, Mataimakin Koci Ya Mutu ana Tsakiyar Atisaye a Ogun

  • Mataimakin kocin kungiyar Shooting Stars, Akin Olowookere ya yanke jiki fadi, ya mutu ana tsakiyar atisaye a jihar Ogun
  • Hukumar gudanarwa ta kungiyar ta yi alhinin mutuwar zakakurin kocin, inda ta bayyana shi da gogagge kuma masanin dabarun kwallon kafa
  • An ruwaito cewa Akin Olowookere ya fadi ne kwatsam ana cikin atisayen yan wasa, kuma an yi kokarin ceto rayuwarsa amma rai ya yi halinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Ƙungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars in (3SC) ta shiga jimami sakamakon rasuwar mataimakin koci da aka naɗa kwanan nan, Akin Olowookere.

Rahotanni sun ce Olowookere, tsohon ɗan wasa kuma tsohon kocin Sunshine Stars, ya fadi ne kwatsam da safe a ranar Litinin, kuma rai ya yi halinsa.

Mataimakin kocin Shooting Stars, Akin Olowookere.
An shiga jimami a filin atisaye da mataimakin koci ya rasu a Ogun Hoto: @Shootingsc
Source: Twitter

Kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars ta tabbatar da faruwar wannan lamari a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Sanatan da ke shirin neman takarar shugaban kasa ya rasu a Colombia

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin koci ya rasu a wurin atisaye

Sanarwar ta ce Olowooiere ya mutu ne yayin atisaye a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode, Jihar Ogun, lokacin da tawagar ke shirin buga wasa na biyu a gasar ValueJet Cup 2025.

An ce ya yanke jiki ya a fadi ana cikin atisaye, aka yi gaggawar ba shi taimakon farko sannan aka garzaya da shi wani asibiti, inda likitoci suka tabbatar ya rasu.

Kungiyar Shooting Stars ta yi ta'aziyya

Sanarwar ta ce:

"Cikin matuƙar bakin ciki da alhini, ƙungiyar Shooting Stars Sports Club tana sanar da rasuwar ƙocinta, Akin Olowokere, wanda ya fāɗi kwatsam kuma ya rasu a filin wasa da safiyar yau, 11 ga Agusta 2025.
"Koci Olowokere ba kawai kwararre ko gogaggen masanin ƙwallon ƙafa ba ne, shi jagora ne, aboki, kuma tamkar uba ga ’yan wasa da mutane da dama.
"Mutum ne da ya nuna tausayi a cikin ɗan gajeren lokacin da ya shafe tare da mu. Baya ga haka, bai taba gajiya ba wajen kokarin haɓaka nasarar tawagarmu.

Kara karanta wannan

Sanata ya cire fargaba, ya tona wadanda suke daukar nauyin kisan mutane a Filato

"Muna miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa, abokan aiki, ’yan wasa, da dukkan masoyan ƙwallon ƙafa a Najeriya a wannan lokaci na jimami. Allah Ya ji kansa.
An yi rashi a tawagar kwallon kafa ta Shooting Stars.
Kungiyar Shooting Stars ta yi ta'aziyyar mataimakin koci Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Takaitaccen tarihin marigayi Olowokere

A lokacin da yake taka leda a Sunshine Stars, ya yi suna saboda jajircewa, ladabi da kuma iya taka leda, rahoton Daily Trust.

Bayan ya yi ritaya daga buga wasa, ya shiga aikin horarwa, inda ya jagoranci Ekiti United sannan ya zama mataimakin koci ƙarƙashin Edith Agoye a Sunshine Stars, kafin daga bisani ya koma Shooting Stars a matsayin jami’in fasaha.

Olowookere mutum ne mai natsuwa amma mai ƙaunar wasan ƙwallon ƙafa, kuma ana girmama shi saboda himmarsa wajen horar da 'yan wasa.

Tsohon dan wasa, Peter Rufai ya mutu a Legas

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta yi jimami kan rasuwar tsohon mai tsaron gida, Peter Rufai.

Rahotanni sun nuna cewa Peter Rufai ya rasu a birnin Lagos sakamakon wata jinya da ya dade yana fama da ita.

Peter Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Najeriya a gasar cin kofin Afrika ta 1994 da kuma shiga gasar cin kofin duniya karo na farko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262