'Mutane Sun Yi Takansu': Halin da Ake ciki a Borno bayan Boko Haram Ta Kashe Sojoji
- Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji, sun yi garkuwa da ɗalibar sakandare sun kuma kona gidaje, motoci da motoci a Borno
- Shugaban ƙungiyar ci gaban Kirawa ya ce irin bala'in da mutanen kauyen Kirawa suka gani ya tilasta su tserewa daga gidajen su
- Har zuwa yanzu ba a sako yarinyar da aka sace ba, yayin da wasu 'yan garin suka nemi mafaka a kauyukan da ke ƙasar Kamaru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Yawancin mazauna ƙauyen Kirawa da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno sun tsere zuwa Kamaru bayan wani harin Boko Haram.
A yayin harin, an ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe sojoji da dama tare da yin garkuwa da wata ɗaliba mai suna Aisha Muhammad.

Source: Twitter
'Yan Boko Haram sun kai hari kauyen Borno
Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa harin, 'yan ta'addan da suka shafe sa’o’i suna barin wuta, sun kai harin ne a daren ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tabbatar da faruwar harin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya ce mazauna kauyen da dama sun bar gidajensu.
“Eh, muna da masaniya kan harin da aka kai ranar Asabar. Sai dai har yanzu babu cikakkun bayanai ba saboda har yanzu mutanen da suka tsere ba su koma gidajensu ba. Don haka ba za mu iya tabbatar da wadanda abin da ya faru da su ba."
- ASP Nahum Daso.
Shi ma shugaban kungiyar ci gaban kirawa, Yakubu Mabba Ali Kirawa, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje, shaguna da motoci.
Mutane sun tsere bayan kisan sojoji
Yakubu Ali Kirawa ya ce:
“Da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Asabar, mayakan Boko Haram suka shigo garin. Sun yi musayar wuta da dakarun hadin sojoji na hadin gwiwa da ke yankin.
“Bayan harin, sun yi garkuwa da wata yarinya mai suna Aisha Muhammad Aja, sannan suka ƙone gidaje, motoci, da shaguna.
“Har sai da ƙarfe 1:00 na dare ne suka bar garin, inda mazauna kauyen suka tsere zuwa Kamaru. Wasu daga cikin mutanen sun dawo, amma wasu ba su dawo ba."
Shugaban kungiyar ya ce yanzu an samu dan kwanciyar hankali a garin yayin da wasu da suka kaura suke ci gaba da dawowa a hankali.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara tura sojoji zuwa yankin don hana sake kai hare-hare.

Source: Original
Halin da ake ciki bayan wannan hari
Majiyar ta ƙara da cewa, iyalai da dama sun rasa gidajensu, yayin da wasu ke neman mafaka a kauyukan da ke kusa da su a Kamaru.a suka sace ba.
“Sun kashe sojoji kuma sun yi garkuwa da ɗalibar sakandare, ajin ta biyu,” a cewar majiyar.
Majiyar ta ƙara da cewa, iyalai da dama sun rasa gidajensu, yayin da wasu ke neman mafaka a kauyukan da ke kusa da su a Kamaru.
Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, domin bai ɗaga kiran waya ba kuma bai maido da kiran ba.
Sojoji sun ragargaji mayakan Boko Haram
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna a lokacin da suke tafiya cikin daji a hanyarsu ta kai hari.
An ce bayan sun gasa masu aya a hannu, dakarun sojojin sun kuma kwato makamai da kayayyaki daga hannun miyagun 'yan ta'addan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


