Abubakar Shekau ya gudu zuwa Kolofata a Kamaru – Kwamandan Boko Haram da aka kama
- Kwamandan Boko Haram da aka kama, Abdullahi Bello, yace sojoji sun yi nasarar kora shi da sauran kwamandoji daga dajin Sambisa
- Rundunar sojin Najeriya ta sanya kyautar naira miliyan uku akan Abubakar Shekau
Wani babban kwamandan Boko Haram, Abdullahi Bello wanda aka fi sani da Abu Zainab, wanda rundunar soji suka kama a ranar 14 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa shugaban yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, Abubakar Shekau ya tsere zuwa Kolofata dake kasar Kamaru.
Sahara Reporters ta rahoto daga majiyar sojoji cewa an kama Abu Zainab ne a Bauchi yayinda yake kokarin guduwa Kano. Kwamandan da aka kama ya fada ma sojoji cewa sojoji sun yi nasarar kora shi da sauran kwamandoji daga dajin Sambisa sakamakon Operation Deep Punch 2 da suke gudanarwa.
KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya na gudanar da wani gagarumin aiki a dajin Sambisa
A halin yanzu, rundunar sojin Najeriya tace zata ba da naira miliyan 3 a matsayin kyauta ga duk wanda ya ba da bayanin da zai kai ga kama shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng