Biki Bidiri: An Daura wa Jaruma Rahama Sadau Aure a Jihar Kaduna

Biki Bidiri: An Daura wa Jaruma Rahama Sadau Aure a Jihar Kaduna

  • Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta shiga sahun matan aure, inda aka daura aurenta da Ibrahim Garba a yau Asabar a Kaduna
  • ‘Yan uwan Rahama sun tabbatar da lamarin ta hanyar wallafa bidiyon taya murna a shafukan sada zumunta a yayin bikin da ya samu halartar ‘yan uwa da abokai
  • Masu kaunar jarumar daga fannoni daban-daban sun yi mata addu’o’i na samun zaman lafiya, hakuri, da dorewar soyayya a tsakanin ma’auratan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga sabon babi na rayuwa bayan da aka daura mata aure da angonta Ibrahim Garba.

Lamarin ya kasance abin farin ciki ga masoyanta da abokan aikinta, inda hotuna da bidiyo suka fara yaduwa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

An daura wa jaruma Rahama Sadau aure a Kaduna
An daura wa jaruma Rahama Sadau aure a Kaduna. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa a Facebook cewa an daura auren ne a jihar Kaduna a yau Asabar, 9 ga Agusta, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahama ta samu yabo daga mashahuran mutane a masana’antar fim da wajen ta, wadanda suka bayyana jin dadinsu game da wannan sabon mataki da ta dauka.

Kafafen sada zumunta sun cika da sakonnin taya murna daga abokan sana’a, ‘yan uwa, da masoya, wadanda suka yi fatan Allah Ya albarkaci zaman auren nata.

Tarihin Rahama Sadau a Kannywood

Rahama Ibrahim Sadau, wacce aka haifa a Kaduna, ta shahara a masana'antar fim ta Kannywood a Najeriya.

Ta samu shahara sosai bayan fitowa a fim din “Gani ga Wane” a shekarar 2013, wanda ya bude mata kofar shigowa cikin masana’antar Kannywood.

Baya ga fitowa a fina-finai, Rahama ta yi fice a matsayin mai shirya fina-finai, inda ta ci gaba da fadada aikinta zuwa fannonin Nollywood da wasu shirye-shirye.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun titsiye Sarki a dajin Zamfara, ya amsa tambayoyi masu zafi

Wannan sabon aure ya nuna wani sabon mataki a rayuwarta bayan dogon lokaci tana cikin harkar fim.

Jaruma Rahama Sadau kafin a daura mata aure
Jaruma Rahama Sadau kafin a daura mata aure. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

An taya Rahama Sadau murnar aure

DW Hausa ta wallafa a Facebook cewa kanwar Rahama, Teemah Sadau ta taya jarumar murna a yau Asabar, haka ma Zainab Sadau ta yi irin haka.

Wannan ya kara tabbatar da cewa an daura auren cikin farin ciki da goyon bayan 'yan uwanta a jihar Kaduna.

Qaseem Haruna Aliero ya yi mata addu’ar samun zaman lafiya, yana mai fatan marasa aure suma su samu abokan rayuwa.

Ali Abdullahi Bako ya ce:

“Allah ya sa alheri, Allah ya ba su zaman lafiya,”

Auone Ibro ya bayyana cewa ya yi fatan mahaifinta na raye don ya shaida wannan rana, kasancewar mahaifin jarumar ya rasu kwanakin baya.

Suleiman Abubakar Funtua ya nuna fatan cewa sauran ‘yan mata a masana’antar Kannywood za su koyi darasi daga Rahama su gane cewa aure ya fi komai muhimmanci.

Kara karanta wannan

Jiragen yaki sun kona 'yan bindiga kurmus suna bikin aure a dajin Zamfara

Ana bikin auren Davido a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa a makon da muke ciki ake cigaba da bikin daurin auren fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke.

Ana bikin auren mawakin da aka fi sani da Davido Chioma Rowland a kasar Amurka, kuma gwamnan Osun ya hallara wajen.

Mawakin ya bayyana cewa ya kashe makudan kudi da suka kai Dala miliyan 3.7, adadin da ya haura Naira biliyan 5.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng