Davido: Mawakin Najeriya Ya Yi Auren Kece Raini, Ya Kashe Sama da Naira Biliyan 5
- Shahararren mawaki Davido ya bayyana cewa ya kashe Dala miliyan 3.7 wajen shirya bikin aurensa da Chioma Rowland
- Wannan biki na zuwa ne bayan na gargajiya da aka yi a Lagos a watan Yuni 2024, kuma ya samu halartar gwamna Ademola Adeleke
- Dangantakar ma’auratan ta gamu da kalubale a baya, ciki har da rashin ɗansu Ifeanyi a 2022, kafin su yi aure har su haifi tagwaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa ya kashe Dala miliyan 3.7 wajen shirya bikinsa da Chioma Rowland.
Adadin kudin da aka kashe ya haura Naira biliyan 5.5 kuma ya jawo ce-ce-ku-ce da jinjinawa daga masoya da jama’a a kafafen sada zumunta.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa bikin da suke yi ya biyo bayan na gargajiya da aka gudanar a watan Yuni 2024 a jihar Lagos, wanda ya samu halartar fitattun mutane daga sassa daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun a watan Afrilu ne mawakin ya sanar da cewa zai gudanar da wannan biki a watan Agusta 2025, amma bai bayyana takamaiman ranar ba.
Yadda aka yi bikin Davido a kasar Amurka
The Guardian ta wallafa cewa an ga mawakin tare da Chioma suna shiga jirgin sama na ƙasa da ƙasa.
Wani rahoto ya ce an kawata jirgin da furanni da kujera mai ɗauke da rubutun “MRS” a matsayin alamar shirin bikin.
Bikin da suka yi a Amurka na zuwa ne bayan mawakin da matar tasa sun gudanar da bikin gargajiya a Lagos, wanda ya tara manyan baki da masoya.
A wannan lokaci kuwa, sun zabi Miami a matsayin wurin da suka kulla muhimmiyar al’adagw ta aure a idon duniya.

Asali: Facebook
Gwamnan Osun ya halarci auren Davido
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, wanda dan uwa ne ga Davido, ya isa ƙasar Amurka domin halartar bikin.
Kakakin gwamnan, Olawale Rasheed, ya tabbatar da tafiyar ta shi bayan wasu tambayoyi daga jam’iyyar adawa ta APC kan inda gwamnan yake.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Kola Olabisi ya tabbatar da zancen a wani jawabi da ya fitar.
Tarihin alakar Davido da Chioma
Soyayyar Davido da Chioma ta fara jan hankalin jama’a tun 2019 lokacin da mawakin ya yi mata tayin aure.
Duk da haka, dangantakar ta shiga cikin rikici a 2021 bayan rahotannin zargin shakuwa da wata mata daban.
A watan Oktoba 2022, suka fuskanci babban bakin ciki bayan rasuwar ɗansu na fari, Ifeanyi, wanda ya nutse a wani gida a Lagos.
Bayan wannan rashin, a watan Maris 2023, Davido ya bayyana cewa sun haifi tagwaye a Amurka a watan Oktoba 2023.
An yi aure 'ya'yan jagoran Izala a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren daya daga cikin manyan jagororin kungiyar Izala, Sheikh Yakubu Musa a Katsina.
Auren ya samu halartar manyan malamai da suka hada da shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Rahoto ya nuna cewa mataimakin Sheikh Sani Yahaya Jingir, Sheikh Yusuf Yusuf Sambo ya halarci bikin daurin auren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng