Masu Sayar wa Ƴan Ta'adda Bindigogi Sun Gama Guje Guje, Sun Shiga Hannu a Kaduna

Masu Sayar wa Ƴan Ta'adda Bindigogi Sun Gama Guje Guje, Sun Shiga Hannu a Kaduna

  • Jami’an ‘yan sandan Kaduna sun cafke mutane biyu a Kurmin-Kogi, bisa zargin saye da sayar da bindigogi ga 'yan ta'adda
  • Wadanda ake zargi, Isah Bello da Sa’idu Haruna, sun kai jami’an tsaro mabuyarsu a cikin daji inda aka gano bindigogi daban daban
  • A wani samame, an kama wani barawon babura, wanda ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar barayin babura da ke addabar Giwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Jami'an rundunar 'yan sandan Kaduna sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi suna sayar da bindigogi ga 'yan ta'adda.

An samu nasarar kwato bindigogi takwas, ciki har da mai kamar AK47 guda hudu da aka kera a gida da kuma 'pistol' hudu, kirar gida.

'Yan sanda sun kama masu sayar wa 'yan ta'adda bindigogi a Kaduna
Jami'an 'yan sanda sun kai samame Soba, inda suka kama dillalan bindigogi. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

An kama masu dillancin makamai a Kaduna

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

DSP ya ce jami'an rundunar sun kai samame tare da cafke wadanda ake zargi ne bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansu.

A cewarsa, jami'an 'yan sanda na ofishin Ikara sun kai samame kauyen Kurmin-Kogi a ranar 5 ga Agusta, 2025, bayan samun rahoton masu safarar makamai.

Wannan samamen ne ya kai ga nasarar cafke mutane biyu da ake zargi — Isah Bello da Sa'idu Haruna, wadanda dukkaninsu 'yan kauyen Damdami ne da karamar hukumar Soba.

"Wadanda aka cafken sun jagoranci jami'ai zuwa mabuyarsu da ke cikin wani daji, inda aka gano bindigogi takwas da aka hada su a gida."

- DSP Manisr Hassan.

Yadda aka gano bindigogi 8 a Soba

Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda ake zargin, Isah Bello, ya yi kokarin tserewa kuma ya ji wa wani jami'in dan sanda ciwo a kokarin hakan, wanda ke samun kulawa yanzu a asibiti.

Jaridar Vanguard ta rahoto sanarwar rundunar na cewa:

Kara karanta wannan

An kama boka mai ba 'yan ta'adda maganin bindiga da kayan tsafi

"A ranar 5 ga Agustan 2025, misalin karfe 2:00 na rana, jami'an 'yan sanda na Ikara suka kai samame kauyen Kurmin Kogi, suka kama mutane biyu, Isah Bello da Sa'idu Haruna, dukansu 'yan kauyen DamDami, gundumar Richifa, karamar hukumar Soba, bisa zargin sayar da bindigogi.
“Wadanda ake zargin sun kuma kai ‘yan sanda inda suka boye kayayyakinsu a cikin daji, inda aka samo bindigogi takwas kirar gida.”
Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama wani kasurgumin barawon babura a Kaduna
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An cafke kasurgumin barawon babur

A wani samame na daban da aka yi a ranar 7 ga watan Agusta, ‘yan sandan sashen Dan Magaji sun kama Shamsudeen Haruna daga Galadimawa a karamar hukumar Giwa, bisa zargin sa da satar babura.

“An cafke wanda ake zargin ne a lokacin da yake ƙoƙarin sayar da baburan sata a wata kasuwar mako-mako.
"An kwato babura 4 daga hannun shi. Ya amsa cewa yana cikin wata shahararriyar kungiyar barayin babura da ke addabar Zariya, Giwa, da kewaye."

- DSP Manisr Hassan.

DSP Hassan ya ƙara da cewa bincike ya kai ga kama wani da ake zargi da sayen baburan satan, wanda ke taimakawa ‘yan sanda a binciken da ake ci gaba da yi.

An kama jami'an tsaro zai sayar da makamai

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta a garin Raan, an rasa rayukan ƴan bindiga 30

A wani labarin, mun ruwaito cewa, DSS ta kama wani jami’in tsaro da ke sayar da makaman gwamnati ga ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

An kama jami’in tare da wasu mutum 53 da suka haɗa da ‘yan bindiga, masu safarar makamai da iyalan wasu masu garkuwa a yayin samame a jihar.

Gwamna Uba Sani ya yaba da nasarorin DSS karkashin sabon Darakta-Janar, Oluwatosin Ajayi, kan yadda suka ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com