Obi: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Je Bauchi, Ya Ba Makarantar Islamiyya Kyautar N5m

Obi: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Je Bauchi, Ya Ba Makarantar Islamiyya Kyautar N5m

  • Peter Obi ya ba da kyautar N15m ga kwalejin jinya da makarantar islamiyya a Bauchi domin tallafa wa fannin kiwon lafiya da ilimi
  • Yayin da ya ce yana ziyartar akalla makarantun jinya 70 a shekara, Peter Obi ya ce malaman jinya su ne ginshikin al'umma
  • Shugabannin makarantun Malikiya da Intisharu sun gode wa Obi, tare da alkawarin amfani da kudin don inganta harkokin karatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya yi abin alheri a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas.

An rahoto cewa Peter Obi ya ba da kyautar Naira miliyan 15 ga kwalejin fasahar aikin jinya da kuma makarantar islamiyya ta Intisharu da ke Bauchi.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar malaman Kano zai nemi gwamna, zai kara da Abba a 2027

Peter Obi ya ba da kyautar N15m ga kwalejin jinya da makarantar islamiyya a Bauchi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a 2023, Peter Obi ya ziyarci Bauchi. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Peter Obi ya ba makarantun Bauchi N15m

Jaridar Punch ce ta ruwaito cewa jagoran 'yan Obidient din ya bayar da kyautar miliyoyin kudi ga makarantun biyu ne a ziyarar da ya kai Bauchi ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa Peter Obi ya ba da kyautar Naira miliyan 10 ga makarantar aikin jinya ta Malikiya yayin da makarantar islamiyyar ta samu kyautar Naira miliyan biyar.

Da yake jawabi a makarantar kwalejin jinyar, dan takarar shugaban kasar ya ce malaman jinya sun dade suna taka rawa a fannin kiwon lafiya na kasar.

Obi ya fadi tasirin malaman jinya

Peter Obi ya bayyana cewa:

"Kuna da matukar muhimmanci ga al'umma, ku babbar kadara ce ga wannan kasa tamu Najeriya, don haka, za mu yi duk mai yiwuwa don ganin mun tallafa maku.
"A yau, kowa ya gane cewa fanni na farko da ke nuna nasarar kowacce kasa shi ne kiwon lafiya, kuma ba za ka samu ingantaccen kiwon lafiya ba idan ba ka ingnta rayuwar masu aikin jinyar ba."

Kara karanta wannan

Daliban Yobe sun samu tagomashi, gidauniyar Atiku ta dauki nauyin karatunsu

"Malaman jinya suna da matukar amfani. Malamin jinya ne ya san ciwon marar lafiya, ya ke kula da marar lafiya har ya warke, don haka malaman jinya su ne komai a gare mu."
Peter Obi ya ce yana ziyartar makarantun jinya akalla 70 duk shekara yana ba su tallafi
Tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya, Peter Obi. Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Tallafin Obi ga makarantun jinya a jihohi

A kowace shekara, Peter Obi ya bayyana cewa yana kai ziyara akalla makarantun koyar da aikin jinya 70 a fadin kasar nan, a cewar rahoton Vanguard.

Ya ce duk makarantar da ya ziyarta, yana ba da tallafin kudi ko na kayan aiki daidai karfinsa, a wani shirinsa na tallafawa kiwon lafiya na shekara-shekara.

Da suke martani kan sha-tara-ta-arziki da Obi ya yi masu, shugabannin makarantar sun jinjinawa da dan takarar shugaban kasar.

Shugaban makarantar Malikiya, Aminu Danmaliki da shugaban makarantar Intisharu, Alhaji Usman Abubakar sun yi alkawarin amfani da kudin wajen ci gaban makarantunsu.

Peter Obi ya ziyarci Sambo Rigachikun

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi, ya kai ziyara wajen Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a jihar Kaduna,

Sanarwa daga shafin Sheikh Rigachikun ta bayyana cewa an tarbi Peter Obi cikin girmamawa, inda aka ba dan siyasar kyautar hula da babbar riga.

A cikin hotunan da aka yada, an hango fitattun mutane ciki har da fitaccen malami, Sheikh Alkali Abubakar Salihu daga Zaria da wasu manyan mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com