Kwankwaso ya kaddamar da makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kano a ranar murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Kwankwaso ya kaddamar da makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kano a ranar murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa

A ranar Litinin, 21 ga watan Oktoban 2019, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaddamar da makarantar koyon aikin jinya da ungozoma a mahaifarsa ta garin Kwankwaso dake karamar hukumar Madobin jihar Kano.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, sabuwar kwalejin da tsohon sanatan shiyyar Kano ta tsakiya ya kaddamar, ya yi amfani da sunan mahaifiyarsa wajen rada mata suna, wato dai Nafisa College of Nursing and Midwifery, Kwankwaso.

Bikin kaddamar da sabuwar kwalejin ta mata zalla na daya daga cikin wasu muhimman shagulgula na bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan na Kano wanda ya cika shekaru 63 a duniya.

Da ya ke gabatar da jawabai kamar yadda ya saba a koda yaushe, Kwankwaso ya ce shawarar assasa kwalejin ba ta wuce ganin masu aikin jinya da kuma ungozoma sun bai wa gwamnati gudunmuwar inganta harkokin kiwon lafiya a jihar ba.

A yayin da sabuwar kwalejin zata kafa tubalin farko da dalibai hamsin kuma tuni aka fara sayar da fam din neman shiga, Sanata Kwankwaso ya ce bude makarantar na daya daga cikin akidunsa na bai wa harkokin ilimi tallafi da kuma inganta jin dadin rayuwar al'umma a jihar Kano.

A cewar tsohon gwamnan, wadanda suka cancanta ne kadai za su samu damar shiga kwaljein a bisa tafarki da kuma tsare-tsaren da hukumar aikin jinya da ungozoma ta shimfida a kasar.

KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta ki amincewa da kasafin kudin ma'aikatar Neja Delta

A nasa jawaban, shugaban kwalejin, Malam Abdullahi Isma'ila, ya ce kaddamar da wannan sabuwar makaranta zai cike wani gurbi na tazarar da ke tsakanin Kudu da Arewacin kasar nan.

Malam Isma'ila ya ke cewa, a farkon shekarar 2019 da muke cikinta, akwai kimanin makarantun koyon aikin jinya da ungozoma 126 a Kudancin Najeriya yayin da 83 kacal suka kasance a Arewa duk da yawan al'umma da ke yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa, yayin bikin kaddamar da sabuwar kwalejin a garin Madobi, an kuma gabatar da wani littafi mai lakabin 'akidar Kwankwasiyya a ci gaban siyasar Najeriya', wato dai ‘Kwankwasiyya in Nigeria’s political Development', wanda Farfesa Sharif Ghali na jami'ar Abuja ya wallafa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel