Ana Batun Yunwa, Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Ton 42,000 na Hatsi a Raba wa Jihohi

Ana Batun Yunwa, Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Ton 42,000 na Hatsi a Raba wa Jihohi

  • Gwamnatin tarayya ta karyata cewa akwai tsananin matsin tattali da yunwa a Najeriya, tana mai cewa abin bai yi muni haka ba
  • Mai ba shugaban kasa shawara, Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnati ta fitar da ton 42,000 na hatsi da aka raba wa jihohi
  • Da yake magana kan farfadowar Naira, Dare ya ce shirye-shiryen gwamnati da dama sun kare 'yan kasar daga yunwa da tsadar rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A baya bayan nan ne wata kafar watsa labarai (ba Legit Hausa ba) ta fitar da rahoto kan tsananin yunwa da matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya.

A cewar kafar, bisa ga wani rahoton UNICEF, talauci, tsadar rayuwa, yunwa da matsin tattali sun munana tsakanin Yuni zuwa Agusta, 2025, rahoton da gwamnati ta ce "an zuzuta."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi martani mai zafi, ta ce ana zuzuta batun yunwa a Najeriya

Fadar shugaban kasa ta yi bayani game da kokarin da take yi na kare tattalin arziki da yunwa
Gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi don magance matsalar yunwa a kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Ahmad Sabo/Facebook
Source: UGC

Matakan gwamnati wajen samar da abinci

Mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai da sadarwa, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X cewa halin da Najeriya take ciki bai yi muni yadda ake tunani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunday Dare ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta riga ta dauki duk wasu matakai da suka dace na ganin hasashen UNICEF bai tabbata ba, kuma ta ga amfanin hakan.

"Akwai matakai da dama da gwamnati ta dauka domin ganin Najeriya ba ta shiga cikin tsananin matsin tattali da yunwa da aka yi hasashe ba.
"Daga cikin matakan akwai fitar da sama da ton 42,000 na hatsi daga rumbun ajiya na tarayya don rabawa jihohi, sannan yanzu haka ana kan sayo karin ton 117,000 na hatsin.
"Hakazalika, shugaban kasa ya kaddamar da majalisar tsaron Abinci ta kasa, kuma an riga an aiwatar da tallafin abinci mai gina jiki a Borno, Yobe, Adamawa, Katsina, Sokoto, da Bauchi."

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi maganar halin da ake ciki, ya ɗauko tarihin sama da shekaru 10

- Sunday Dare.

Kokarin gwamnati a daidaita darajar Naira

Ba a iya bangaren abinci ba, Sunday Dare ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai na ganin an samu daidaitaccen tattalin arziki, ta fuskar daidaita farashin canji.

A cewar Sunday Dare, Naira ta yi karfi a kasuwar canji a Agustan 2025, inda ake canza ta kan N1,525/$1 idan aka kwantanta da yadda take a Maris din 2024, lokacin da take N1,800/$1.

Ya dage kan cewa:

"Mun yarda darajar Naira ta fadi warwar, to amma wannan wani tsohon labari ne, domin yanzu tana kan farfadowa."

Ya danganta farfadowar darajar Naira kan karin hada-hadar mai, samun yardar masu zuba jari, daidaituwar kasuwar hannayen jari da kuma biyan bashin kudaden canji na $4bn.

Sunday Dare ya ce gwamanatin tarayya ta dauki duk wasu matakai na daidaita tattalin arziki da samar da abinci
Sunday Dare ya kare gwamnatin Bola Tinubu kan batun yunwa da matsin tattalin arziki. Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

Shirye-shiryen gwamnati na yaki da talauci

Idan aka cire batun samar da abinci da kuma daidaita darajar Naira, mai ba shugaban kasar shawara ya ce Najeriya ta samu ci gaba da fannoni daban daban.

Kara karanta wannan

Wata matsala ta tunkaro Najeriya, za a iya rasa Naira tiriliyan 1.6 duk shekara

Sunday Dare ya karyata cewa an rufe shirin ciyar da dalibai abinci, yana mai cewa har yanzu sama da yara miliyan 9.8 a daga makarantu 53,000 na ci gaba da amfani da shirin.

Ya kuma kara da cewa akwai gidaje sama da miliyan uku da suka samu tallafin N75,000 kowane karkashin shirin tallafi na Renewed Hope CCT, wanda ake sa ran zai amfani mutane miliyan 15, yayin da dalibai sama da 396,000 suka samu tallafin karatu karkashin NELFUND.

Hadimin shugaban kasar ya kuma ce shirin tallafin mazabu na Renewed Hope WDP da aka kaddamar kwanan nan zai zamo miliyoyin mutane a mazabu 8,809 daga talauci.

Tinubu ya ba jihohin tallafin tirelolin shinkafa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da gudummuwar tirelolin shinkafa ga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya ce an bada wannan tallafin ne domin rabawa ƴan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi a matakin yaƙi da yunwa.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar tabbatar da kowane ɗan Najeriya ya samu abincin da zai sa a bakinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com