Tsadar Rayuwa: An Tara Malamai 1000 a Kwara, Za a Yi wa Tinubu Addu'o'i na Musamman
- Fastoci 1,000 daga kungiyar OAIC sun taru a Ilorin domin gudanar da addu'o’i na musamman ga Najeriya da Bola Ahmed Tinubu
- Evangelist Thomas Adeboye ya bukaci ‘yan Najeriya su dage da addu’a don Ubangiji ya ba Tinubu damar gyara tattalin arziki da tsaro
- A cewarsa, Shugaban kasa Tinubu ya nuna kaunarsa ga Najeriya da kuma burinsa na farfado da tattali, don haka yana bukatar addu'o'i
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - An tara akalla fastoci 1,000 da suka fito daga kungiyar majami'u ta Afrika (OAIC) a Ilorin, babban birnin jihar Kwara don yi wa kasa addu'a.
Malaman 1,000 za su hada kai, su kwana su yini suna yi wa Shugaba Bola Tinubu addu'a don ya samu nasarar shawo kan matsalar tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika

Source: Facebook
Shugaban kungiyar OAIC, Evangelist Thomas Adeboye ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Ilorin yayin da yake magana da 'yan jarida, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tara malamai su yi wa Tinubu addu'a
Evangelist Thomas Adeboye ya ce abin takaici ne yadda tattalin arziki da tsaro ke tabarbarewa a kasar, inda ya nemi 'yan Najeriya su dage da addu'a.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya nuna kaunarsa ga Najeriya da kuma burinsa na farfado da kasar daga doguwar sumar da ta yi ta kowanne fanni.
Babban malamin addinin Kiristan ya ce lallai Najeriya na bukatar taimako daga kowanne dan kasa, musamman ta fuskar yin addu'ar kawo sauki.
"Najeriya na bukatar addu'a a kan 'yan bindiga, tabarbarewar tattalin arziki da kuma siyasar kasar da ke kokarin dagulewa.
"Ya zama wajibi mu gudanar da addu'a ta musamman ga Shugaba Tinubu da gwamnoni, mu roki Ubangiji ya ba su basirar mulki, ya kuma yi riko da hannayensu."
- Evangelist Thomas Adeboye.
An ba Tinubu da gwamnoni shawarwari
Jaridar Tribune ta rahoto Evangelist Adeboye ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya samar da tsare tsare da za su kawo sauki ga rayuwar talakawan kasar nan.
Ya bayyana cewa:
"Muna sane da cewa da shi da gwamnoni suna kokari. Duk da haka, muna bukatar su rika kawo tsare-tsaren da za su sanya da yawan 'yan Najeriya farin ciki."

Source: Facebook
Malamin addinin Kiristan ya ce an shirya duba lafiyar wadanda za su halarci wannan gangamin addu'ar kyauta, inda za su iya ganawa da likitocin ido, ciwon sukari da sauran cutuka.
Evangelist Thomas Adeboye ya ce malaman da za su hadu domin yin addu'o'in za su shiga halwar ganawa da Ubangiji, suna masu mika lamuransu gare shi, domin ya karba daga rokonsu.
A cewarsa, OAIC za ta kuma karrama mutanen da suka nuna goyon bayansu ga ayyukan kungiyar ta hanyar ba su kyaututtuka da addu'o'i na musamman.
Sarki ya tara malamai kan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya shirya taron addu'a domin neman taimakon Allah a halin da ake ciki a ƙasar nan.
Sarkin ya haɗa manyan maluman addinin musulunci a fadarsa kuma an yi addu'o'in neman zaman lafiya da samun nasarar shugabanni.
Wakilan gwamnatin jhar Kwara sun halarci wurin addu'ar da aka yi wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

