Karya Ta Kare: DSS Ta Kama Shugaban 'Yan Ta'addan Mahmuda da Suka Bulla Najeriya

Karya Ta Kare: DSS Ta Kama Shugaban 'Yan Ta'addan Mahmuda da Suka Bulla Najeriya

  • Wasu rahotanni sun ce DSS ta kama shugaban kungiyar ta’addanci ta Mahmuda kusa da iyakar Jamhuriyar Benin
  • Mazauna Baruten da kewaye sun ce an jima ba a ji duriyar shugaban 'yan ta'addan ba, wanda ya haddasa rudani a sansanin su
  • An yaba wa shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro bisa wannan nasarar da ake ganin za ta dawo da zaman lafiya a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Wasu mazauna jihohin Kwara da Neja, musamman a yankunan da ke iyaka da Jamhuriyar Benin sun yi farin ciki da kama shugaban kungiyar Mahmuda.

Mutanen jihohin sun bayyana farin cikinsu bisa rahotannin da ke cewa jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar ta’addanci ta Mahmuda, Abubakar Mahmuda.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika

Wasu jami'an hukumar DSS a bakin aiki
Wasu jami'an hukumar DSS a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Rahoton da tashar NTA ta wallafa a X ya nuna cewa ana jin tsoron Mahmuda a sassa da dama na Neja da Kwara saboda halinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da babu wata hukuma ta tsaro da ta fito fili ta tabbatar da hakan, wasu mazauna jihar Kwara sun bayyana cewa tun karshen makon da ya gabata babu labarin Mahmuda.

Mahmuda ta bace, babu labarin kungiyar

Bisa ga cewar mazauna yankin, babu wani daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Mahmuda da ya iya bayyana inda shugaban nasu ya tafi.

Wannan lamari ya haddasa rade-radin cewa jami’an DSS sun yi masa kwanton-bauna lokacin da ya ziyarci wani boka da yake yawan zuwa wajensa.

Wasu daga cikin mazauna sun ce jami’an DSS sun kama Mahmuda da ransa, sannan suka garzaya da shi zuwa wani wurin da ba a bayyana ba, lamarin da ya kara rikitar da mabiyansa.

Tashar Arise News ta wallafa cewa ana ganin wannan bacewar ce ta jefa sansanin kungiyar Mahmuda cikin rikici da rashin jagora.

Kara karanta wannan

Wani rikicin ya barke a Filato, an rasa rai bayan kona tarin gidaje

An jinjinawa DSS da shugaba Bola Tinubu

Wani dagaci a yankin Baruten da kungiyar ta shahara da kai hari ya bayyana a tattaunawarsa da manema labarai cewa:

“Mun gamsu da yadda DSS suka yi aikin nan cikin sirri da kwarewa. Wadannan 'yan ta'adda sun dade suna hana mu sukuni.”

Shi ma wani shugaban kasuwar shanu a yankin ya ce:

“Mun gode wa Allah da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda wannan babban nasara. Mun sha zama cikin tsoro, amma yanzu muna da kwarin gwiwar samun zaman lafiya.”
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Tarihin kungiyar Mahmuda a Najeriya

Kungiyar Mahmuda na daga cikin wadanda ke da alaka da kungiyoyin ta’addanci a kasashen Mali da Nijar.

An bayyana cewa kungiyar ta mamaye wani bangare na jihar Neja tun kusan shekaru biyar da suka wuce bayan sun kori masu gadin filin shakatawa na Kainji.

A 'yan watannin baya, kungiyar Mahmuda na kashe mutane da yin garkuwa da su, tare da rusa garuruwa a Kwara da Neja.

Kara karanta wannan

Kwastam: Za a sayar wa 'yan Najeriya litar man fetur a kan N400

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi luguden wuta kan 'yan ta'adda a Zamfara.

Hakan na zuwa ne yayin da aka samu rahoton cewa 'yan ta'addan sun taru domin bikin daurin aure a wani daji.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan wutar da aka yi yayi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin 'yan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng