'Najeriya Ka Iya Wargajewa kafin Zaɓen 2027': Tsohon Minista Ya Yi Hasashe
- Tsohon minista a Najeriya ya yi gargaɗi cewa Najeriya na iya rugujewa kafin 2027 idan ba a aiwatar da wasu sauye-sauye ba
- John Nnia Nwodo ya bukaci a baiwa yankuna ikon mallakar arziki tare da biyan haraji ga tarayya domin kare haɗin kai
- Tsohon shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya soki Bola Tinubu da cewa yana jagorantar tabarbarewar attalin arziki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon ministan yaɗa labarai kuma tsohon shugaban Ohanaeze Ndigbo, Chif John Nnia Nwodo, ya yi gargaɗi kan zaben 2027.
John Nwodo ya ce Najeriya na iya rugujewa kafin zaɓen 2027 matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa na sake fasalin ƙasa ba.

Source: Facebook
2027: Tsohon minista ya gargadi shugabanni
Tsohon ministan ya fadi haka ne yayin gabatar da jawabin bude taro a bikin kaddamar da littattafan Ike Abonyi, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nwodo ya soki tsarin mulkin Najeriya da ya kira "Tsarin bai daya mai siffar tarayya" wanda bai dace da kasar ba.
An gudanar da taron a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, inda fitattun ’yan siyasa suka halarta, ciki har da Peter Obi, Mohammed Hayatu-Deen da wakilin Gwamnan Bauchi, Emmanuel Agbo.
Nwodo ya bukaci a mika ikon gudanar da albarkatu ga gwamnatocin yankuna tare da aiwatar da tsarin kuɗin tarayya domin kauce wa rikicin tsarin mulki.
Ya ce idan ba a aiwatar da wannan sauyin ba kafin 2027, wasu yankuna na iya kauracewa zaɓe ko ƙin amincewa da sakamakon, wanda zai jefa ƙasa cikin rudani.
Ya ce:
“Najeriya dole ta sake fasalin tsarin mulkinta ta baiwa yankuna ikon mallakar albarkatunsu, su na biyan haraji ga tarayya domin kare ayyuka kamar tsaro da shige da fice.
“Idan hakan bai faru ba, ba za mu da wata mafita illa mu rabu da juna."

Source: UGC
Nwodo ya koka da matsin tattalin arziki
Cif Nwodo ya kuma ambaci halin ƙuncin tattalin arziki, rashin aikin yi ga matasa da lalacewar ababen more rayuwa a matsayin alamu na durƙushewar ƙasa, cewar The Guardian.
Ya ambaci rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya na 2025 cewa Najeriya ce ƙasa mai mafi ƙarancin tsawon rai a duniya, shekaru 54.8, da asarar $1bn duk shekara saboda lalatattun hanyoyi.
A jawabinsa, tsohon shugaban PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya zargi Bola Tinubu da jagorantar abin da ya kira "lalacewar dimokuraɗiyya da tattalin arziki".
Secondus ya ce:
“Muna nesa da samun dimokuraɗiyya ta gaskiya. Abin da muke da shi dandalin lashe zaɓe ne kawai. Najeriya na kan hanyar rushewa."
Malami ya hango wanda zai lashe zaben 2027
Kun ji cewa wani malamin gargajiya da ya yi hasashen nasarar APC a 2023, yanzu ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kasa zaɓen 2027.
A wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga malamin yana kulumboto, tare da cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben.
Hasashen malamin dubar ya jawo cece-kuce, yayin da 'yan Najeriya suka zura ido suka ko hasashensa zai zama gaskiyar kamar na baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


