Nnia Nwodo ya girgiza da rashin samun Jami’in kabilar Ibo a jerin hafsun Sojoji

Nnia Nwodo ya girgiza da rashin samun Jami’in kabilar Ibo a jerin hafsun Sojoji

- Jagoran Ohanaeze Ndigbo ya soki Muhammadu Buhari a kan nadin Hafsun Sojoji

- Nnia Nwodo ya soki yadda aka nada Hafsun tsaro ba tare da akwai Jami’in Ibo ba

- Kungiyar Afenifere ta ce nadin da aka yi jiya ya sake nuna son kan shugaban kasa

Tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mutanen Ibo, Nnia Nwodo, ya nuna mamakinsa a game da nadin hafsun sojoji da aka yi.

Cif Nnia Nwodo, ya yi tir da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari na ware mutanen kasar Ibo a mukaman da ya bada a gidan sojan Najeriya.

Jaridar Vanguard ta yi hira da sabon shugaban kungiyar SMBF ta mutanen Kudu da yankin Arewa maso tsakiyan Najeriya, bayan an fitar da sanarwar.

Nnia Nwodo ya nuna cewa Buhari ya nuna lallai bai kaunar Inyamurai tun da ya nada hafsun sojoji ba tare da ya dauko wani soja daya daga kabilar ba.

KU KARANTA: Ka makara wajen nadin shugabannin tsaro - PDP ga Buhari

Jawabin Dattijon na zuwa ne bayan an nada sababbin shugabannin sojoji a ranar 26 ga watan Junairu, 2021.

Ya ce: “Shugaban kasa Muhammadu Buhari mun gode da ka samu alfahari a kasar Ibo a wani karon. Ka nuna cewa ba mu isa mu rike wani bangaren tsaro ba”

Bayan wannan magana, jaridar ta ce Nwodo bai sake cewa komai game da wannan nadi da aka yi ba.

Haka zalika sakataren yada labarai na kungiyar Afenifere, Yinka Odumakin ya shaida wa jaridar Punch cewa Buhari ya makara wajen yin wannan nade-nade.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka sallami Hafsoshin soja - Buhari

Nnia Nwodo ya girgiza da rashin samun Jami’in kabilar Ibo a jerin hafsun Sojoji
Ana zargin Shugaban kasa Buhari da nuna son-kai wajen nadin Hafsun Sojoji
Asali: Depositphotos

Yinka Odumakin ya koka da cewa babu wani jami’in soja daga Kudu maso gabashin Najeriya da ya samu kujera a wannan nadin shugabannin sojojin da aka yi.

Za a ga ko da babu sojan da aka zaba daga Kudu maso gabas, sabon shugaban duka hafsun tsaron kasar, Janar Lucky Irabor ya fito ne daga yankin Kudu maso kudu.

Shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro kuma ya nada wasu ne bayan koke-koken jama'a.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar kungiyoyi irinsu PANDEF ta mutanen yankin Neja-Delta ta ji dadin wannan nadi da aka yi, akasin matsayar kungiyar Afenifere.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel