An So a Tashi Gari, Ƴan Sandan Kaduna Sun Gano Bam aka Ɓoye a Kayan Gwangwan

An So a Tashi Gari, Ƴan Sandan Kaduna Sun Gano Bam aka Ɓoye a Kayan Gwangwan

  • Rundunar ƴan sandan Kaduna ta kama bama-bamai da makamai da aka shigar jihar a cikin kayan gwangwan
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, Rabiu Muhammad ya bayar da umarnin rufe kamfanin da aka gano bama-baman
  • Ya kuma haramta wa masu sana'ar jari bola karɓar kayan gwangwan daga yankunan da ke fama da rikice-rikice

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta gano wasu bama-bamai da ba su fashe ba tare da tarin makamai da aka boye cikin kayan gwangwan da aka kawo daga Borno.

Lamarin ya tayar da hankula, musamman ganin yadda ake shigo da kaya daga yankunan da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda.

An kama bama-bamai a Kaduna
Yan sanda sun kama bama-bamai daga Borno Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Daily Trust, mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an gano kayan ne a ranar 2 ga watan Agusta, 2025, bayan samun bayanan sirri daga sahihan majiyoyi.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An shiga wurin da ake bauta, an kashe mutumi ɗan shekara 45

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun gano bama-bamai a Kaduna

Jaridar Punch ta wallafa cewa an gano abubuwan fashewar ne a wani kamfanin kayan gwangwan da ke yankin masana’antu na Kudandan, a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

A cikin sanarwar rundunar ta ce:

“Ƙwararru daga sashen fashewar abubuwa (EOD), ƙarƙashin kwamandan sashen, sun garzaya wurin da abin ya faru. Bayan cikakken bincike, an tabbatar da cewa abubuwan da ake zargi bamabamai ne da ba su fashe ba.”

Ƙwararrun jami’an EOD sun kwashe bama-baman zuwa wani wuri na musamman domin tarwatsasu cikin kwarewa da bin ka’idojin tsaro.

Ƴan sandan Kaduna sun gano makamai masu haɗari

A yayin gudanar da binciken, ƴan sandan sun gano wasu makamai da suka haɗa da bindigu ɗauke da harsashi guda shida.

Sai kuma ƙarin harsashi 15 masu girman 7.2mm da wasu bindigu guda 3 da wasu nau’ukan harsashi daban-daban.

Biyo bayan wannan lamari, Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, ya bada umarnin rufe kamfanin nan take.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da basaraken Zamfara yana tsaka da ƙoƙarin barin gari

Taswirar jihar Kaduna
Yan sanda sun hana shigo da gwangwan daga Arewa maso Gabas Hoto: Legit Hausa
Source: Original

An yi haka ne domin ba wa jami’an EOD damar kammala bincike da tabbatar da babu wasu bamabamai da suka rage a wurin.

Ya ce:

“Dukkannin kamfanonin tattara shara da dakunan ajiya a fadin jihar su daina karɓar kaya daga wuraren da ke fama da rikici, musamman daga Arewa maso Gabas.”

CP Rabiu ya ƙara da cewa an umarci kwamandojin yankuna da DPOs su kama duk wanda ya karya wannan umarni.

Ƴan sanda sun gano bama-bamai a Kano

A baya, mun wallafa cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da gano karin bama-bamai tara a kamfanin karafa na Yongxing a unguwar Mariri.

An yi nasarar gano makaman ne bayan an samu fashewar ban da ta hallaka mutane biyar yayin da wasu ke gadon asibiti a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta.

DSP Hussaini Abdullahi, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana cewa bayan fashewar da ta auku, an gano bama-bamai guda bakwai a wurin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng