Yaki Zai Kare: Bello Turji Ya Ajiye Makamai bayan Haduwa da Malaman Musulunci
- Bello Turji ya amince da dakatar da kai hare-hare kan manoma tare da sakin mutane 32 da ya yi garkuwa da su a dajin Zamfara
- Malamin Musulunci, Sheikh Asadus-Sunnah, ya ce malamai sun gana da Turji har sau uku a cikin watan Yuli domin samun zaman lafiya
- Biyo bayan lamarin, an samu sassaucin zaman lafiya a yankin Shinkafi, inda jama’a ke komawa gona cikin kwanciyar hankali
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Fitaccen jagoran 'yan ta'adda na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Bello Turji, ya mika wasu daga cikin makaman sa tare da sako mutane 32 da ya yi garkuwa da su.
Hakan na zuwa ne bayan ganawar sulhu da wasu malaman Musulunci a dajin Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi.

Kara karanta wannan
'Sau 3 muna zama da Turji a wata 1': Shehin malami ya ja hankalin hukumomi kan sulhu

Source: Twitter
Sheikh Musa Yusuf wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan a wani bayani da ya yi a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zaman lafiya na cigaba da tabbatuwa a yankin tun bayan amincewar Turji da wasu abokan aikinsa wajen dakatar da hare-hare, musamman kan manoma da ke shan wahala a dajin.
An gana da Bello Turji sau 3 a Yuli
Premium Times ta wallafa cewa malamin ya bayyana cewa jama’ar Shinkafi ne suka neme su a matsayinsu na malamai su tunkari Turji domin ya bar mutane su koma gonakinsu.
Ya ce sun gana da Turji da wasu abokansa kamar Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila, inda duk suka amince da shirin zaman lafiya.

Source: Facebook
Turji ya saki mata da yaran da ya kama
Asadus-Sunnah ya ce bayan ganawar su da Turji, an samu nasarar sakin mutane 32 da suka hada da mata da yara da suka kwashe wata hudu a daji.
Ya ce wasu daga cikin matan sun haifi 'ya’ya a cikin daji, inda kuma wata daga cikinsu ta sha wahala sakamakon cizon maciji.
An nuna bidiyon lokacin da aka sako mutanen da irin wahalar da suka sha wajen barin dajin Bello Turji.
An samu kwanciyar hankali a Shinkafi
Sheikh Asadus-Sunnah ya ce tuni jama’a sun fara koma gona a Shinkafi ba tare da tsoron sace su ba, yana mai cewa malamai na ci gaba da shawo kan Turji ya rungumi zaman lafiya gaba ɗaya.
Sai dai ya ce ba su bukaci ya mika dukkan makaman sa ba domin kada hakan ya sanya ya zama abin farmaki ga wasu kungiyoyin da ba sa goyon bayan zaman lafiya.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, mai ba da shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, Gwamna Dauda Lawal da Sanata Shehu Buba bisa goyon bayan da suke bai wa hanyar zaman lafiya.
An kashe mace, an kona gidaje a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa an samu wani sabon rikici a jihar Filato da ya yi sanadiyyar mutuwar wata mace guda daya.
Baya ga haka, rahotanni sun nuna cewa rikicin ya yi sanadiyyar kona gidajen mutane a wasu yankuna na jihar.
Dakarun sojin Najeriya sun isa wajen da ake rikicin tare da kwantar da hankalin jama'a bayan jaddada cewa za a gano masu laifin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

