Daliba daga Yobe Ta Yi Bajinta, Ta Yi Fata Fata da Ƙasashen Turawa 69 a Gasar Turanci

Daliba daga Yobe Ta Yi Bajinta, Ta Yi Fata Fata da Ƙasashen Turawa 69 a Gasar Turanci

  • Matashiyar daliba ‘yar jihar Yobe, Nafisa Abdullah Aminu, ta lashe gasar Turanci ta duniya, inda ta doke dalibai daga ƙasashe 69
  • Nafisa ta wakilci Najeriya a gasar 'TeenEagle' ta 2025 da aka gudanar a London, kuma ta bayyana matsayin ilimi mai inganci da ke Najeriya
  • Iyalan Nafisa sun yaba da taimakon gwamnati da makarantar NTIC, suna cewa nasararta hujja ce kan irin ƙarfin ɗaliban Najeriya a duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, Birtaniya - Wata daliba daga jihar Yobe ta ba da mamaki a cikin Turawa yayin wata gasa da aka gudanar a birnin London.

Dalibar da ake kira Nafisa Abdullah Aminu mai shekaru 17 daga jihar Yobe a Najeriya, ta lashe gasar ƙwarewar Turanci.

Daliba daga Yobe ta doke Turawa a gasa
Daliɓa daga Yobe yi wuji-wuji da Turawa a gasar Turanci. Hoto: Auwal Y Umar.
Asali: Facebook

Daliba daga Yobe ta farantawa yan Najeriya rai

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Rahoton Daily Trust ya ce dalibar ta lashe gasar ce ta duniya da ake kira 'TeenEagle' 2025 a London da ke Birtaniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nafisa ta wakilci Najeriya ta hanyar makarantar 'Nigerian Tulip International College' (NTIC), Yobe, inda ta kayar da sama da ɗalibai 20,000 daga ƙasashe 69.

Ciki har da dalibai daga ƙasashen da Turanci ke zama harshensu na asali, wanda hakan ke nuna ƙwazon Nafisa da ingancin ilimin Najeriya.

Yobe: Iyalan dalibar sun yi magana kan Nafisa

Hakan na cikin wata sanarwa da daya daga cikin shugabanni a dangin dalibar, Hassan Salifu, ya bayyana.

Hassan ya ce nasarar Nafisa ta faru ne daga jajircewarta da kuma kulawar gwamnati da ta samu.

Ya bayyana jin dadinsa da kuma nuna godiya musamman kulawar da Nafisa ta samu daga gwamnatin Mai Mala Buni da kwarin guiwa daga yan uwanta.

Ya ce:

“Nasarar da ‘yarmu ta samu a duniya ba za ta yiwu ba ba tare da irin goyon bayan Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ba."

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata

Iyalan daliba a Yobe sun jinjina mata
An yabawa daliba a Yobe bayan doke Turawa a gasar Turanci. Hoto: Legit.
Asali: Original

Musabbabin samun nasarar daliba Nafisa a Turai

Sanarwar ta ce nasarar ta jawo alfahari ga iyali, makaranta, jihar da ƙasa baki ɗaya bisa irin gagarumar nasarar da ta samu.

Iyalan sun yaba da ƙoƙarin kwalejin NTIC wajen ba da ilimi mai inganci da tallafawa dalibai su kai matakin da duniya ke yaba musu, Leadership ta tabbatar.

Sannan suka buƙaci gwamnatoci su yaba da nasarar, suna cewa wannan hujja ce da ke nuna cewa ɗaliban Najeriya na iya fice a duniya.

Wasu na ganin cewa idan aka ba su ingantaccen yanayi da tallafi, ɗaliban Najeriya na iya gogayya da sauran ƙasashen duniya a fannoni da dama.

Dalibi Musulmi ya lashe gasar 'Bible' a Lagos

A baya, mun ba ku labarin cewa wani yaro Musulmi mai shekaru 9, Muritala Desmond, ya lashe gasar Littafi Mai Tsarki ta makarantu da 'Bible Society of Nigeria' ta shirya a Lagos.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rikita jiga jigan APC a taro, ya taka rawa a waƙar 'Omologo' ta Rarara

Desmond, ɗalibi a 'Salem Baptist International School', ya ci maki 100 duk da rashin goyon bayan kakarsa da bambancin addininsa.

Hukumar BSN ta bukaci goyon bayan jama’a don ci gaba da shirya irin waɗannan gasa da kuma bai wa yara tallafi da kyaututtuka saboda kara musu kwarin guiwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.