Gwamna Uba Sani Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, Ya Sauya Mukaman Kwamishinoni

Gwamna Uba Sani Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, Ya Sauya Mukaman Kwamishinoni

  • Gwamna Uba Sani ya sauya mukaman kwamishinan shari’a da na tsaro da harkokin cikin gida domin inganta ayyukan a Kaduna
  • Yayin da aka dage Sule Shuaibu daga ma’aikatar shari'a zuwa ta tsaron cikin gida, James Kanyip ya zama sabon babban lauyan jiha
  • Uba Sani ya bukaci kwamishinonin su zage damtse wajen kawo sauyi a yaki da ‘yan bindiga da gyaran shari’a a jihar Kaduna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa, inda ya musanya mukaman wasu kwamishinoni biyu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Litinin.

Gwamnan Kaduna ya sauya wa kwamishinoni 2 mukamai
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Kaduna: An sauyawa kwamishinoni wurin aiki

Jaridar Punch ta rahoto cewa Uba Sani ya sauya wa kwamishinan shari’a, Sule Shuaibu (SAN), mukami zuwa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida.

Kara karanta wannan

2027: Malamin addini ya hango kujerar gwamnoni 7 da ke fuskantar barazana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

James Kanyip (PhD), wanda shi ne kwamishinan tsaron cikin gidaa baya, yanzu ya zama sabon babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na Kaduna.

Ibraheem Musa ya bayyana cewa an yi sauye-sauyen ne don karfafa ingancin aiki a ma’aikatun ta hanyar amfani da gogewar kwamishinonin.

“Gwamna Uba Sani ya umurci manyan jami’an biyu da su sanya gaskiya da jajurcewa wajen tafiyar da sababbin mukaman da aka ba su," inji Ibraheem Musa.

Sharhin masana kan sauya kwamishinonin

Gwamnan, a cewar sanarwar, ya nuna kwarin gwiwa cewa duka mutanen biyu za su yi amfani da gogewarsu a ma'aikatun da aka kai su, yana mai jaddada cewa yi wa al'umma aiki na kwarai shi ne ginshikin gwamnatinsa.

A cewar sanarwar:

“Gwamnan ya bukaci kwamishinonin su yi amfani da dimbin gogewarsu da iliminsu a sababbin ayyukansu. Ya yi addu'ar Allah ya yi musu jagoranci kuma ya yi riko da hannayensu.

Ko da yake an bayyana sauye-sauyen a matsayin “karamin garambawul,” masana siyasa sun ce sauya mukaman ya shafi ma’aikatu biyu mafi muhimmanci a jihar.

Kara karanta wannan

Dilan ƙwaya: Bayanai sun bulloƙo kan kwamishinan Kano, ana zargin ya karbi $30,000

An ce ma’aikatar shari’a da ta tsaron cikin gida sun taka muhimmiyar rawa a yakin da gwamnati take yi kan ‘yan fashi, satar mutane, da kuma sauyi a fannin shari’a.

Gwamna Uba Sani ya ce yana da yakinin kwamishinonin da ya sauya wa wurin aiki za su kawo ci gaba a Kaduna
Gwamnan Kaduna, Uba Sani yana jawabi a wani taro na sake bude wata babbar kasuwa da aka rufe a jihar. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Sanarwar gwamnatin Kaduna kan garambawul

Wani bangare na sanarwar Ibraheem Musa ya ce:

“An san Sule Shuaibu, babban lauyan gwamnati da zurfin ilimi kan shari’a kuma ya jagoranci sauye-sauye a fannin shari’ar jihar Kaduna a baya.
“Komawarsa ma’aikatar tsaron cikin gida ya sanya shi a sahun gaba wajen daidaita harkokin tsaro na jihar, musamman ma a kan batun karuwar ‘yan fashi a yankunan karkara da rikice-rikicen kabilanci.
“A gefe guda kuma, Dakta James Kanyip, ya kasance gogaggen masanin shari’a kuma tsohon mataimakin shugaban ma’aikatan gwamna.
“Ana sa ran aikinsa na baya a fannin sasanta rikice-rikicen al’umma da manufofin tsaro zai ba da cikakkiyar fahimtar sabon mukaminsa na babban lauyan gwamnati."

Uba Sani ya nada sababbin kwamishinoni

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Uba Sani ya yi nadin sababbin kwamishinoni domin inganta shugabanci a jihar Kaduna.

Sanata Uba Sani ya nada Farfesa Abubakar Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimi, sai aka sauyawa Farfesa Sani Bello ma’aikata

Gwamnan ya ce yana sa ran sababbin kwamishinonin za su kawo sauyi a ma’aikatunsu tare da samar da hanyoyin magance matsalolin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com