Ruwa Zai Yanke: NiMet Ta Saki Sunayen Jihohi 6 da Za Su Fuskanci Fari a Agusta
- NiMet ta bayyana cewa ruwan sama da ya wuce kima zai sauka a jihohin Arewa 10 da suka hada da Sokoto, Zamfara a watan Agusta
- Yayin da ta ce za a samu saukin ruwa a Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce akwai yiwuwar jihohin Kudu maso Yamma su fuskanci fari
- An shawarci jama’a da hukumomi da su shirya don tunkarar ambaliya, cututtuka da sauran abubuwan da ruwan Agusta zai zo da su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Yayin da Najeriya ke shiga tsakiyar daminar bana, hukumar NiMet ta fitar da sabon rahoto na hasashen yanayi na watan Agusta 2025.
A cikin rahoton, NiMet ta gargadi al’umma game da karuwar ruwan sama, yiwuwar ambaliya da kuma cututtuka masu nasaba da sanyi a wasu yankuna.

Asali: Original
Ruwa mai kima da fari a jihohin Najeriya
A cikin rahoton da aka fitar a shafin NiMet na X a ranar Litinin, hukumar ta bayyana cewa za a samu saukar ruwan sama da ya wuce kima a wasu jihohin Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin Arewacin Najeriya da za su fuskanci ruwan sama da ya wuce kima sun hada da Sokoto, Zamfara, Jigawa, Katsina, Yobe, Borno, Kebbi, Kano, Bauchi da Gombe.
Wannan karin ruwan saman na iya janyo ambaliya mai tsanani musamman a yankunan da ke bakin koguna da yankunan da ke gangare, a cewar NiMet.
Sai dai, rahoton ya nuna cewa za a samu karancin ruwan sama a wasu sassan Taraba, Kudancin Adamawa da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A yankin Kudu maso Yamma kuwa, NiMet ta yi hasashen za a samu fari a farkon watan Agusta, amma za a samu dawowar damina daga baya.
Gargaɗin NiMET ga hukumomi da jama’a
NiMet ta bukaci hukumomin ba da agajin gaggawa da su kasance cikin shiri, su kuma yi amfani da rahotannin sauye-sauyen yanayi don hana asarar rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Adamawa da jihohi 7 za su fuskanci ambaliya daga Litinin zuwa Laraba
Ta shawarci al’ummomin da ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan faruwa da su dauki matakan kariya kamar adana muhimman takardu da kadarori a cikin kayayyakin da ruwa ba zai iya lalata wa ba.
"Ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a yi zai jawo koguna su cika su tumbatsa har su yi amai, kuma dama an san ruwan Agusta na yawan kawo ambaliya mai tsanani."
- Hukumar NiMet.

Asali: Original
An ba iyaye shawara kan kiwon lafiya
Rahoton ya kuma nuna yiwuwar saukar sanyi a lokacin daddare da kuma safiya, wanda zai iya shafar lafiyar yara kanana da dattijai.
An shawarci iyaye da su rika rufe ‘ya’yansu da kaya masu dumi, tare da karfafa garkuwar jiki ta hanyar cin abinci mai gina jiki da sinadarin Vitamin C domin kare su daga mura da sanyi.
Ga matafiya da direbobi, an ja kunnen su da su guji bin hanyoyi ko gadoji da ruwa ya rufe, musamman bayan ruwan sama ya sauka.
NiMet ta shawarci manoma da su rika bin shawarwarinta wajen yanke shawara game da shuka da girbi, tare da kauce wa aikin gona a filayen da ruwa ya mamaye don kare lafiyarsu da amfanin gona.
Ambaliya ta yi barna a jihohin Arewa 3
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mamakon ruwan sama ya jawo rushewar gidaje da cinye gonaki a jihohin Bauchi, Filato da Neja.
A Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta.
A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng