Arewa maso gabashin Nigeria na iya fuskantar matsanancin Fari da yunwa, Majalisar dinkin duniya

Arewa maso gabashin Nigeria na iya fuskantar matsanancin Fari da yunwa, Majalisar dinkin duniya

  • Arewa maso gabashin Nijeria na iya fuskantar kalubalen rashin abinci
  • Wannan na kunshe a cikin jawabin da ofishin kodinatan bada agaji na majalisar dinkin duniya ya saki ranar Alhamis
  • A cewar jawabin mata da kananan yara na cikin wanda abin yafi shafa

Akalla mutane milyan hudu da rabi a Arewa maso gabashin Nijeria na gabar fuskantar kalubalen rashin abinci, a cewar majalisar dinkin duniya.

A wani jawabi da ofishin kodinatan bada agaji na majalisar ya saki ranar Alhamis, abin ya tsananta a arewa maso gabashin kasar, rahoton AriseNews.

Idan ba agaji aka kaiwa jihohi irinsu Borno, Adamawa da Yobe ba, to mutane zasu sha wahala wurin neman abinda zasu ciyar da kansu a wannan yanayin ha'ulai na shekarar 2021.

A jawabin wanda ya ta'allaka da kimar gwajin abinci na watan Maris 2021, ya bayyana cewa kusan mutane 4.4m wanda suka hada da yan gudun hijira, zasu fuskanci karancin abinci.

Kara karanta wannan

Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

Sannan wasu mutane 775,000 suna kan gabar fuskantar matsanancin fari, wanda shine mafi tsanani a cikin shekaru hudu.

Jawabin ya kara da cewa kungiyar masu bada agaji, majalisar dinkin duniya da kungiyoyi masu zaman kansu sun hada karfi da karfe wurin bayyana yadda yunwa take kara ta'azzara a arewa maso gabashin kasar, kuma suna aiki hannu da hannu a kowani mataki na gwamnatin tarayya dana jihohi.

Arewa maso gabashin Nigeria na iya fuskantar matsanancin Fari, Majalisar dinkin duniya
Arewa maso gabashin Nigeria na iya fuskantar matsanancin Fari, Majalisar dinkin duniya Source: Twitter
Asali: Twitter

Da yake magana a cikin jawabin, kodinatan majalisar dinkin duniya kan bada agaji, Edward Kallon ya bayyana cewa:

"Kungiyar bada agaji ta matukar damuwa akan ta'azzarar yunwa a arewa maso gabashin Nijeria.
Rashin abinci a yau har ya kai matakin yadda yake a 2016-2017, lokacin da abin ya fi kamari. Majalisar dinkin duniya da masu zaman kansu na aiki hannu da hannu da gwamnatin tarayya domin a dakile wannan matsanancin Farin."

Ya kara da cewa

"Mata a kauyukan da abin ya shafa sun labarta yadda ya'yansu ke kwana suna kuka saboda tsananin yunwa."

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Yace abin zai iya tsananta lokacin damina idan ba,a magance cutuka kamar Amai, gudawa da malaria ba.

A cewar jawabin, rashin tsaro da ya addabi arewa maso gabashin kasar, tsananin ruwa, ambaliya na cikin abubuwan da suke hana manoma zuwa gonakinsu domin su shuka abinda za'a ci.

Magance rashin abinci yana bukatar shiri mai tsawo na musamman wanda ya kunshi barin mutane suyi rayuwa ta samun ingantaccen noma da taimaka musu wurin basu hannun jari da kayan noman.

Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe

A wani labarin kuma, Akalla mutum 70 ne aka ce sun rasa rayukansu a garin Jebbu Miango da Kwall na karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau sakamakon harin yan bindiga.

Kaakin kungiyar cigaba Irigwe, Davidson Malison, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda yan ziyara suka ziyarci wajen da aka kai harin.

Ya ce an kashesu ne lokacin hare-haren da aka kwashe kwanaki hudu tun ranar Asabar zuwa Laraba ba tare da taimakon yan sanda ko wasu jami'an tsaro ba.

Kara karanta wannan

Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng