Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda 2 da Ke Tsaron Wani Ɗan Majalisa
- A yankin Okigwe da ke jihar Imo, 'yan bindiga sun kashe wasu 'yan sanda biyu a wani hari da ya jefa al'umma cikin fargaba da rudani
- An ce 'yan sandan da aka kashe suna rakiyar shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Ebonyi ne lokacin da miyagun suka rutsa su
- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta tura jami'ai don kamo 'yan bindigar da suka aikata laifin, kuma ta sha alwashin gurfanar da su a kotu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Mazauna yankin Okigwe da ke jihar Imo sun shiga cikin tashin hankali a ranar Lahadi lokacin da 'yan bindiga suka kashe wasu 'yan sanda biyu.
An ce 'yan bindigar sun yi wa 'yan sandan kwanton bauna a yankin da aka ce yana da hatsari, inda suka bude masu wuta nan take.

Source: Facebook
Abin da ya kai 'yan sanda Okigwe
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa 'yan sandan da ke ba da kariya ga shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ebonyi, Kingsley Ikoro ne aka farmaka.
Wasu majiyoyi sun ce an kashe 'yan sanda biyu a ranar Lahadin, yayin da suke yiwa dan majalisar rakiya, kuma hanya ta bi da su ta Okigwe.
Daya daga cikin motocin da ke a tawagar dan siyasar ce ta samu matsala, wanda ya sa 'yan sandan suka tsaya a wajen yayin da sauran tawagar ta yi gaba.
Yayin da ake kokarin gyara motar da ta lalace, miyagun 'yan bindigar sun fito daga wurin da suke buya, suka bude wuta kan 'yan sandan, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'ai biyu.
'Yan sanda sun magantu kan farmakin
An ruwaito cewa yankin Okigwe na jihar Imo ya kasance wata mafakar miyagun mutane, kuma an sha samun hare-hare a yankin.

Kara karanta wannan
Mutanen gari da 'yan sanda sun yi arangama da 'yan sanda a Abuja, an samu asarar rai
Jaridar Punch ta rahoto cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, a ranar Litinin, ya sha alwashin cewa za a kamo wadanda suka kashe jami'an.
"Babu inda za su je su iya tserewa hukuma, lallai za su girbi abin da suka shuka," a cewar Henry Okeye.

Source: Facebook
An fara farautar wadanda suka yi kisan
Kakakin rundunar ya kuma ce an kwashe gawarwakin jami'an 'yan sandan da aka kashe a bakin aiki zuwa dakin ajiye gawa, kuma za a gudanar da cikakken bincike kan mutuwarsu.
Henry Okeye ya kara da cewa an tura kwararrun 'yan sanda zuwa yankin da abin ya faru, kuma sun fara farautar 'yan bindigar.
Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta sha alwashin kamo wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da cewa sun girbi abin da suka shuka.
Fusatattun mutane sun hallaka DPO a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fusatattun matasa sun farmaki ofishin 'yan sanda a Kano, bayan mutuwar wani matashi a hannun rundunar.
Shugaban ofishin 'yan sandan Rano (DPO) ya gamu da ajalinsa bayan ya samu munanan raunuka a yayin harin, wanda ya jawo aka kona motoci.
Rundunar 'yan sanda ta kama mutum 27 da ake zargi da kai harin, yayin da kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
