Dangote Ya Bude wa 'Yan Najeriya Guraben Neman Aiki a Kamfaninsa
- Kamfanin Dangote ya sanar da buɗe guraben aiki sama da 30 ga ‘yan Najeriya da suka cancanta a sassa daban-daban
- Ana neman ma’aikata a sassa irin su wuraren sarrafa abinci, samar da siminti da sauran rassan kamfanin attajirin
- Daga cikin guraben da aka buɗe akwai shugabannin sassa, ma’aikatan tsaro, injiniyoyi da masu kula da jigilar kaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kamfanin Dangote ya sanar da fara ɗaukar sababbin ma’aikata a wurare sama da 30 a rassan kamfanin da ke faɗin ƙasar.
Wannan mataki yana daga cikin kokarin kamfanin wajen bai wa matasa dama da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Source: UGC
Legit ta tattaro bayanai kan yadda Dangote zai dauki ma'aikata ne a wani sako da kamfaninsa ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa ana iya neman aikin ta shafin yanar gizonsu a nan.
Dangote na neman ma’aikata daban-daban
Dangote ya bayyana cewa buɗe guraben aikin ya shafi manyan kamfanoninsa kamar kamfanin samar da siminti da abinci, inda ake buƙatar ƙwararru a fannoni daban-daban.
A cikin jerin guraben aikin da aka bayyana akwai kananan ma'aikata a sashin jigilar kaya na masana’antar siminti da ke Ibese da sauransu.
Haka zalika, ana neman jami'in da zai rika kula da jigilar kaya kamfanin siminti mallakar Aliko Dangote.
Sauran guraben sun haɗa da masana harkar gas na CNG da jami'an tsaro a masana’antar siminti ta Obajana.
The Cable ta rahoto cewa daga cikin guraben da kamfanin ya buɗe akwai:
- Karamin jami’in jigilar kaya a masana’antar siminti ta Ibese
- Shugaban sashen ajiya da jami’in hulɗa da ma’aikata
- Jami’in tabbatar da karɓa da tsara isar da kaya
A bangaren kamfanin siminti akwai:
- Mataimakin shugaban sashen kula da na’urorin lantarki
- Babban jami’i mai kula da injinan ruwa
- Mataimakin babban jami’i mai kula da injinan wuta
- Kwararre kan kula da injinan iskar gas (CNG)
- Manajan kula da gyaran manyan motoci
- Jami’an tsaro
A bangaren Dangote Foods kuma, ana neman:
- Mai sarrafa injin juya sinadarai
- Manajan kula da abokan hulɗa a yankuna
- Jami'in kula da abokan hulɗa

Source: UGC
Dangote na rage zaman kashe wando
Kamfanin Dangote ya kasance ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikata da dama a fadin Najeriya da ma nahiyar Afirka gaba ɗaya.
Kamfanin ya ce yana ƙoƙarin cika alkawuran da ya dauka na samar da dama ga ‘yan ƙasa, da kuma bunƙasa kasuwanci da rayuwar jama’a.
Ana bukatar masu neman aikin su ziyarci shafin kamfanin domin neman cikakken bayani game da kowanne matsayi da za su nema.
Matatar Dangote za ta sayar da hannun jari
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta fitar da sanarwar cewa nan gaba kadan za ta fara sayar da hannun jari.
Attajirin nahiyar Afrika, Aliko Dangote ne ya bayyana hakan da kan shi a wani taron makamashi da aka yi a Abuja.
Alhaji Aliko Dangote ya kara da cewa matatar shi za ta cigaba da samar da makamashi, musamman gas domin inganta harkar girki a gidajen Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

