Shugaban NNPCL Ya Yi Murabus saboda Zargin Satar N34bn? Majiya Ta Fayyace Gaskiya
- Wata majiyar fadar shugaban kasa ta karyata rahoton cewa Bayo Ojulari ya yi murabus daga shugabancin NNPCL
- Wasu kungiyoyin fararen hula sun zargi Ojulari da hannu a badakalar $21m tare da kira ga EFCC da ICPC a kama shi
- Sai dai, wasu kungiyoyi sun kare Ojulari, inda suka ce ana yi wa shugaban NNPCL ɗin bita da kulllin siyasa ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Ba gaskiya ba ne rahotannin da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo ke yadawa cewa Bayo Ojulari, shugaban kamfanin NNPCL, ya yi murabus daga mukaminsa.
Wani amintaccen majiyar fadar shugaban kasa ya bayyana wa manema labarai a ranar Asabar cewa wannan rahoto “karya ne kuma sharri ne kawai.”

Asali: Twitter
Shugaban NNPCL bai yi murabus ba
Rahotannin sun yi zargin cewa hukumar EFCC ce ta tilasta wa Ojulari yin murabus daga kujerar shugabancin NNPCL, a cewar jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai majiyar fadar shugaban kasa ta karyata wannan batu, tana mai cewa babu gaskiya ko kadan a cikin wannan ikirari.
Shugaba Bola Tinubu ne ya nada Bayo Ojulari a watan Afrilu, 2025, tare da umarnin ya aiwatar da sauye-sauyen da za su kara inganta ayyuka, dawo da amincewar masu saka jari da kuma tabbatar da cewa NNPCL ta zama kamfani mai riba da tsari.
Kafin nadin Ojulari, Shugaba Tinubu ya sallami tsohon shugaban kamfanin, Mele Kyari, da shugaban kwamitin gudanarwa na NNPCL, Pius Akinyelure, a wani bangare na kokarinsa na gyara harkokin kamfanin.
Zarge-zargen da ake yi wa shugaban NNPCL
Takaddamar ta samo asali ne daga zargin da ke nasaba da badakalar $21m (kimanin N34.65bn) na cin hanci, inda kungiyoyin fararen hula kamar OilWatch Nigeria da Workers’ Rights Alliance suka bukaci a kama Ojulari tare da gurfanar da shi a kotu.
Kungiyoyin sun danganta wannan bukata da ikirarin cewa wani da ake tsare da shi, Abdullahi Bashir Haske, ya amsa cewa Ojulari ne ya ba shi ajiyar kuɗaɗen.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 31 ga Yuli a hedikwatar EFCC, gamayyar kungiyoyin fararen hula ta zargi Ojulari da cin amanar tattalin arzikin kasa.
Gamayyar ta kuma bayyana cewa rufe matatun mai da aka dade da yi da kuma shirin sayar da kadarorin NNPCL su ne makasudin zanga-zangar da suka yi.
An kwarmata wa EFCC zargin rashawa a NNPCL
Kungiyoyin sun fara zanga-zanga na kwanaki uku tun daga 1 ga watan Agusta a gaban majalisar tarayya, hedikwatar NNPCL da ofisoshin EFCC don tilasta gwamnati daukar mataki.
Wasu karin zarge-zarge sun bayyana cewa akwai wani tsarin karbar cin hanci na $21m tsakanin masu cinikin mai da kwangilolin bututun mai, wanda aka gano bayan Ojulari ya sauya tsarin karbar kudade a kamfanin.
Jaridar Pubch ta rahoto cewa wani mai kwarmato ne ya sanar da EFCC waɗannan bayanai, wanda hakan ya sa aka toshe asusun da ake zargi da hannu a cikin badakalar.

Asali: Twitter
Kungiyoyi sun samu sabani kan shugaban NNPCL
A watan Mayun 2025, kungiyar SERAP ta bukaci EFCC da ICPC su binciki zargin kin sanya Naira biliyan 500 a cikin asusun tarayya daga watan Oktoba zuwa Disamba na shekarar 2024.
Duk da haka, wasu kungiyoyi kamar CGGCI da HURIWA sun kare Ojulari, suna masu zargin cewa an shirya zanga-zangar ne kawai don cimma muradun siyasa.
Duk da haka, masu suka sun nuna damuwa kan kashe makudan kudade ba bisa ka’ida ba a NNPCL, ciki har da wani taron horo mai tsada a Kigali da aka ce an je da jiragen haya, da kuma yanayin aiki mai tsanani da ya janyo murabus na ma’aikata.
N210trn: Shugaban NNPCL ya samu matsala da majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sanatoci sun bukaci shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.
Majalisa ta bayyana takaici a kan bambancin kuɗi na Naira tiriliyan 210 da aka samu daga rahoton asusun kamfanin mai na kasa.
Bayan rashin bayyanar Ojulari a gabanta, majalisar dattawan ta yi barazanar cewa za ta iya sawa a kamo shi, sannan a mika shi kotu.
Asali: Legit.ng