Amnesty Int'l Ta Dura kan Tinubu da Gwamnati Ta Ƙi Tsoma Baki Shekaru 6 da 'Sace' Dadiyata

Amnesty Int'l Ta Dura kan Tinubu da Gwamnati Ta Ƙi Tsoma Baki Shekaru 6 da 'Sace' Dadiyata

  • Kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty International ta bayyana takaici a kan shirun gwamnati shekaru shida da ɓatan Abubakar Dadiyata
  • Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun ɗauke matashin ɗan gwagwarmayar a gidansa a ranar 2 ga watan Agustan 2019 a garin Kaduna
  • Rahotanni sun ce tun bayan wannan lokaci, babu wanda ya sake ji daga gare shi ko ma labarin inda ya shiga ballantana a san halin da ya ke ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta duniya, Amnesty Int'l, ta nuna damuwa kan ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Dadiyata, wanda malami ne a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, ya shahara a kafafen sada zumunta wajen wallafa ra’ayoyinsa kan siyasa da rayuwar yau da kullum.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin ministan Tinubu da Gwamna, an ci gyaran Bago kan matakinsa

Amnesty ta fusata kan Dadiyata
Amnesty Int'l ta kalubalanci gwamnati a kan Dadiyata Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

Jaridar DW Hausa ta ruwaito, Dadiyata ya ɓace ne tun ranar 2 ga watan Agusta, 2019, bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga gidansa a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan da su ka tafi da shi a daren ranar, ba a sake ji daga gare shi ko kuma halin da ya shiga.

Amnesty ta kalubalanci gwamnatin Tinubu

BBC Hausa ta ruwaito shugaban Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya bayyana damuwar ƙungiyar kan yadda gwamnatin Bola Tinubu ke ci gaba da yin gum game da ɓacewar Dadiyata.

Sanusi ya yi wannan jawabi ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a jihar Kaduna a ranar Asabar.

Ya nanata cewa akwai matuƙar damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke kin daukar mataki kan lamarin ko yunƙurin binciko inda ya shiga.

Dadiyata: Kiran Amnesty Int'l ga Tinubu

Isa Sanusi ya bayyana cewa jama’a da dama na cikin fargaba kan yanda ake nunawa mutane barazana saboda bayyana ra’ayinsu a fili.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

Ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike mai zaman kansa tare da bayyana gaskiyar inda Dadiyata yake.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
Amnesty ta soki Tinubu saboda bacewar Dadiyata Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce rashin hoɓɓasar gwamnati kan ɓacewar Dadiyata na kara tsoratar da mutane game da faɗin albarkacin bakinsu ko sukar gwamnati ta kowace fuska.

Ya bukaci gwamnati da ta tabbatar an fitar da cikakken bayani kan halin da Dadiyata ke ciki domin dawo da amincewa da tsarin adalci a ƙasar.

Babu bayanai a kan Dadiyata

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudurinsa na binciko ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda ya ɓace a shekarar 2019.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, lokacin da ya sha rantsuwa kafin hawa kujerar mulki, Gwamna Abba ya ce ba zai bari batun ɓacewar ɗan tafiyar Kwankwasiyya ya tafi a banza ba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa za ta hada gwiwa da dukkanin hukumomin tsaro domin gano inda Dadiyata yake da kuma hukunta masu hannu a ɓacewar sa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng