Dadiyata: Iyaye da Iyali sun koka game da halin tashin hankalin da suka shiga a shekaru 2

Dadiyata: Iyaye da Iyali sun koka game da halin tashin hankalin da suka shiga a shekaru 2

  • A yau aka cika shekaru biyu da aka sace Abubakar Dadiyata a gidansa a Kaduna
  • ‘Ya ‘yan wannan Bawan Allah da mahaifansa suna kewan shi tun a Agustan 2019
  • An shirya taro na musamman a Kano domin addu’ar Allah ya kubuto da Dadiyata

Kaduna - A ranar 2 ga watan Agusta, 2019, wasu mutane da har yau ba a san su wanene ba, suka dauke wani matashi da ake kira Abubakar Idris, Dadiyata.

A yau Litinin aka shafe shekaru biyu da sace Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata ko kuma Abu Hanifa, har yanzu ba a sake jin wani labari a kan shi ba.

BBC Hausa ta yi hira da iyaye da iyalin Dadiyata domin jin halin da ake ciki, amma abin babu dadin ji.

Mai daki da mahaifiyar Dadiyata sun yi magana

Mai dakin Dadiyata da ke rike da ‘ya ‘ya kananan mata biyu ta ce suna cikin masifa sakamakon abin da ya faru da mai gidanta tun daren 2 ga Agustan 2019.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

"Ba karamin tashin hankali muke ciki ba tun da aka sace shi. Har yau ba mu taba cire rai ba."

"Kullum ina sa rai In sha Allahu wata rana zai dawo, har yanzu babu labari. Kullum da daddare idan aka taba kofar shiga gidan sai in ji kamar shi ne ya dawo.”

Mahaifiyar Dadiyata, Fatima Abubakar ta shaida wa manema labarai cewa tun lokacin da wannan abin ya faru, babu wani takamaimen bayani a kan ‘dan na ta.

Dadiyata
Dadiyata Hoto: globalvoices.org
Asali: UGC

Mahaifin Dadiyata ya yi magana, ya na kuka

Malam Danjuma Yero ya ce ‘dansa yaron kirki ne wanda ya ke dawainiya da su a lokacin da yake nan, ya yi bayani yana hawaye, ya roki Ubangiji ya bayyana shi.

Yahaya Usman wanda kawu ne a wurin Dadiyata, ya na fama da larurar shanye war jiki, tun lokacin da wannan labarin ya zo masa, sai ya yanke jiki, ya fadi.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

An yi addu’o’i domin Ubangiji ya bayyana shi

Kungiyar Kwankwasiyya Twitter Guild ta bakin shugabanta, Abdullahi I. Ibrahim ta shirya taro domin yi wa Dadiyata addu’a a Kano bayan komai ya ci tura.

Sahelian Times ta ce kungiyar ta na zargin an cafke Dadiyata ne saboda yana caccakar gwamnati.

'Yan uwa da abokan arziki sun tuntubi ofishin jami'an 'yan sanda da jami’an tsaro masu fararen farin kaya, amma duk sun bayyana cewa matashin bai hannunsu.

Wannan Bawan Allah ya na cikin masu sukar gwamnatin APC a kafefen sada sadarwa na zamani, kuma malamin makaranta ne a wata jami’a ta kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel