Garambawul: Tinubu Ya Kori Shugabar Hukumar NCCC daga Aiki, Ya Nada Sabuwar Shugaba

Garambawul: Tinubu Ya Kori Shugabar Hukumar NCCC daga Aiki, Ya Nada Sabuwar Shugaba

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabar farko ta hukumar kula da sauyin yanayi (NCCC), Dr. Nkiruka Madueke
  • Bayan sallamar Dr. Nkiruka, shugaban kasar ya amince da nadin Mrs. Omotenioye Majekodunmi a matsayin sabuwar shugaba
  • Majekodunmi ƙwararriya ce a harkar sauyin yanayi wadda ke da gogewar shekaru 17 a aiki da hukumomi na ƙasa da na duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaban Bola Tinubu ya sallami Dr. Nkiruka Madueke daga mukaminta na shugabar farko ta hukumar kula da sauyin yanayi ta kasa (NCCC).

Shugaban kasar ya nada Mrs. Omotenioye Majekodunmi a matsayin sabuwar shugabar NCCC domin maye gurbin Dr. Madueke da aka sallama.

Shugaba Bola Tinubu ya sallami shugabar hukumar kula da yanayi ta kasa (NCC)
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ya jagoranci wani taron FEC a ranar 15 ga Yunin 2023. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya sauya shugabar hukumar NCCC

Wannan sauyin shugabancin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar wanda mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya rubuta, ta ce:

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Mrs. Omotenioye Majekodunmi a matsayin sabuwar shugabar hukumar kula da sauyin yanayi ta kasa (NCCC).
“Mrs. Majekodunmi ta maye gurbin Dr. Nkiruka Madueke, shugabar hukumar ta farko da Tinubu ya nada a watan Yunin 2024.

Sanarwar ta ce Mrs. Majekodunmi ƙwararriyar lauya ce a fannin muhalli, kuma masaniya a harkokin tafiyar da kudade na kula da sauyin yanayi, wadda ke da ƙwarewar sama da shekaru 17.

Bayani kan sabuwar shugabar NCCC

An ce ta yi aiki tare da hukumomi na cikin gida da na duniya kan makamashi, harkokin sinadarin carbon, da jagoranci kan sauyin yanayi.

A cewar Onanuga, kafin nadin nata, Majekodunmi ita ce mai ba da shawara ta kuɗi a hukumar NCCC, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin sauyin yanayi na Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga ganawa da ministoci da manyan ƙusoshin gwamnati a Aso Rock Villa

Shugaba Tinubu ya godewa Dr. Madueke da aka sallama bisa sadaukarwar da ta yi na gina tubalin ci gaban hukumar NCCC.

“Nadin Majekodunmi ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin Tinubu wajen ba sauyin yanayi muhimmanci tare da amfani da dabaru wajen bunkasa tattalin arziki, tsaro da walwalar jama’a,” inji sanarwar.
Shugaba Tinubu ya kori Nkiruka Madueke daga shugabancin hukumar NCCC
Dr. Nkiruka Madueke, shugabar farko ta hukumar kula da sauyin yanayi ta kasa (NCCC). Hoto: @NCCCSNigeria
Source: Twitter

Bayani kan ayyukan hukumar NCCC

Hukumar NCCC ita ce cibiyar gwamnatin Najeriya da ke kula da sha’anin sauyin yanayi, wadda aka kafa karkashin dokar sauyin yanayi ta 2021, aka kuma ƙaddamar da ita a 2022 lokacin Shugaba Muhammadu Buhari.

NCCC na kawo tsari tare da aiwatar da dabaru irin su NCCAP, sannan tana kare muradun garuruwa masu rauni ta fuskar sauyin yanayi wajen ganin sauyin bai illata su ba, kamar yadda aka wallafa a a shafin UNCCAP.

A matsayin cibiyar hulɗar Najeriya da yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (UNFCCC), NCCC na haɗa kai da ƙasashen duniya don ganin Najeriya ta cimma manufar rage fitar da gurbataccen hayaƙi nan da 2060.

Sauyin yanayi: Za a dasa itatuwa miliyan 6

Kara karanta wannan

Ana korafi, Tinubu ya ba 'dan Arewa shugaban hukumar kashe gobarar Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu za ta ba tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 aiki karkashi shirin dashen itatuwa miliyan shida.

Karamin ministan muhalli, Dr Iziaq Salako ne ya bayyana hakan, a yayin kaddamar da wani shirin gwamnati na dakile gurbacewar muhalli da sauyin yanayi.

Ministan, ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su goyi bayan shirin ta hanyar dasa itatuwa a gidajensu da garuruwansu don kare muhalli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com