Sauyin yanayi ne ke sa makiyaya daga waje shigowa Nigeria, In ji Ganduje

Sauyin yanayi ne ke sa makiyaya daga waje shigowa Nigeria, In ji Ganduje

- Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya roki gwamnatin tarayya da ta binciki yaduwar makiyayan da ke shigowa cikin Najeriya daga waje

- Ganduje ya ce makiyayan sun fado Najeriya ne saboda canjin yanayin da aka samu

- Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, yayin wani shirin talabijin

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa canjin yanayi na tilasta wa makiyayan kasashen waje shigowa cikin kasar nan.

Channels TV ta rahoto cewa ya ce yawo da dabbobi daga wannan bangare na kasar zuwa wani ba sabon abu bane.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan ya bayyana cewa canjin yanayi ya rage hanyoyin dabobi a kasar, wanda hakan ya sa makiyaya ke shiga gonakin mutane.

Daga ƙarshe: Ganduje ya gano yadda wasu baƙin hauren Fulani ke shigowa Nigeria
Daga ƙarshe: Ganduje ya gano yadda wasu baƙin hauren Fulani ke shigowa Nigeria Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Dattawa sun aika takarda ga Gwamnan CBN, sun ce ana cutar mutanen Arewa

Ya ce:

“Yawo da dabbobi daga wani bangare na kasar zuwa wani ba sabon abu ba ne, hatta daga wasu kasashen da ke makwabta. Bakin makiyayan, saboda canjin yanayi, suna ƙaura zuwa Najeriya tare da dubban dabbobi.

“A lokutan baya, akwai wadatar hanyoyin dabbobi saboda yawan mutane bai habbaka ba kamar yanzu; ayyukan noma saboda yawan jama'a, ba haka yake ba. Amma akwai wuce gona da iri.

"Hatta ga yawan dabbobin da ke shigowa Najeriya daga Afirka ta Yamma ma ya karu saboda yalwar wuraren kiwo a yankin arewa ta tsakiya da kuma kudancin kasar."

Har ila yau, Ganduje ya lura cewa saboda mutane ba za su zauna su zuba ido ana masu barna a filin ba, da yawa daga cikin makiyayan sun sayi makamai don kare kansu.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka

Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da yawaitar makiyayan kasashen waje wadanda a cewarsa, babu hanyar da za a gane su a kasar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance matsalar.

A wani labarin, Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), na reshnen Ekiti, Adamu Abache, ya goyi bayan ayi wa makiyaya rajista.

Alhaji Adamu Abache ya yi kira ga gwamnatin jihar Ekiti, ta yi wa duk makiyayan da ke zama a Ekiti rajista domin aji dadin gane duk wani mai kiwon dabbobi.

Jaridar Vanguard ta ce Adamu Abache ya bukaci ayi wannan rajista ne a kananan hukumomin da makiyaya su ke zaune, su na kiwo ba tare da sun saba doka ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel