Shugaban Iran Ya Gargaɗi Tinubu kan Tsoma Baki a Rikici da Isra'ila? An Samu Bayanai

Shugaban Iran Ya Gargaɗi Tinubu kan Tsoma Baki a Rikici da Isra'ila? An Samu Bayanai

  • An yi ta yada wani faifan bidiyo da ke nuna shugaban Iran yana gargaɗin Najeriya ka da ta tsoma baki a rikicin kasar da Isra’ila
  • An tabbatar da cewa Ebrahim Raisi da aka nuna a bidiyon ya rasu tun a Mayun 2024, kafin rikicin ya fara cikin Yuni 2025
  • Babu wata sanarwa daga shugaba Masoud Pezeshkian ko hukumomin Iran da ke nuna sun yi barazana ga Bola Tinubu ko Najeriya a rikicin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani mai amfani da kafar sadarwa ya saka bidiyo yana cewa shugaban Iran ya gargaɗi Najeriya ka da ta tsoma baki rikicin tsakanin Iran da Isra’ila.

An yi ta yada bidiyon wanda ya fara saka shakku a zukatan wasu mutane duba da abin da ya faru tsakanin Iran da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Jarumin fim, Don Richard ya talauce, yana neman taimakon N30m daga 'yan Najeriya

An samu bayanai kan cewa shugaban Iran ya gargadi Tinubu
Babu gaskiya cewa shugaban Iran ya gargaɗi Tinubu kan tsoma baki a rikicinsu da Isra'ila. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

An binciki batun cewa Iran ta gargadi Tinubu

Sai dai binciken kwa-kwaf na Africa Check ya karyata rahoton da ake yadawa cewa shugaban Iran ya gargadi Bola Tinubu kan tsoma baki a lamuransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon da ake ta haɗawa ya bayyana ne tun a ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2025 da ta gabata.

A cikin bidiyon, mutumin ya ce:

"Labari na gaggawa, Shugaban Iran ya aika da gargaɗi ga Tinubu ka da ya shiga wannan yaki tsakanin Iran, Isra’ila da Amurka.
"Tinubu, me ya sa kake neman yaki da ba za ka iya karewa ba? Iran za ta iya tarwatsa Najeriya da makami ɗaya.
"Wannan gargaɗi ne ga kasashen Afirka. Ka da ku tsoma baki, wannan ba yakinku ba ne. Ku shawarci Tinubu ya janye."

A bidiyon, an saka rubutu da hotunan Raisi da Tinubu, tare da kalmomin turanci kamar haka "Iranian president to Nigeria: ‘Don't involve yourself in this’”.

Kara karanta wannan

ADC: 'Yadda gwamnoni da hadimai ke cika kunnen Tinubu da karya da gaskiya'

Babu tabbacin kan cewa Iran ta gargadi Tinubu
An yi binciken kwa-kwaf kan rahoton cewa Iran ta ja kunnen Tinubu a rikicinta da Isra'ila. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yaushe tsohon shugaban Iran, Raisi ya rasu?

A daidai lokacin da ake yaki tsakanin kasashen a watan Yuni ne mai TikTok ya yi ikirarin cewa Raisi ya gargaɗi Tinubu kada ya tsoma baki.

Sai dai Raisi ya rasu a hatsarin jirgi a ranar 19 ga Mayu, 2024, sama da shekara guda kafin rikicin Yuni 2025.

Saboda haka, shugaban Iran yanzu shi ne Masoud Pezeshkian, ba Raisi ba wanda aka ce ya gargadi Tinubu.

Haka kuma, da shugaban Iran ya yi irin wannan magana ko kiran Najeriya ƙaramar ƙasa, da labarin ya cika kafafen yada labarai.

Har ila yau, da hakan ta faru, da gwamnatin Najeriya ta nuna rashin jin daɗi da irin wannan furuci.

Duk da Tinubu ya fitar da sanarwa da ke kira da zaman lafiya da kokarin kare ’yan Najeriya a Iran, bai yi munanan kalamai kan kasar ba.

Saboda haka, wannan magana da ake cewa shugaban Iran ya yi gargaɗi ga Tinubu ba gaskiya ba ce.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya cika alkawarin samar da tsaro a Najeriya, an kafa hujja da jihohi 2

Iran ta fitar da gargadi ga Amurka, Isra'ila

Kun ji cewa jagoran addini na Iran, Ayatollah Khamenei, ya jagoranci bikin tunawa da sojojin da Isra’ila ta kashe a yakin da suka yi.

Khamenei ya bayyana cewa sojojin sun bar gagarumar gudunmawa mai daraja ga kasar Iran da al’ummar Musulmi.

Ya soki Amurka da Isra’ila, yana mai cewa suna kin hadin kai da ci gaban kimiyya da addini a kasar Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.