Kyautar N1bn: Ƴan Gudun Hijira Sun Ɓarke da Zanga Zanga bayan Ziyarar Matar Tinubu

Kyautar N1bn: Ƴan Gudun Hijira Sun Ɓarke da Zanga Zanga bayan Ziyarar Matar Tinubu

  • 'Yan gudun hijira sun mamaye titin Makurdi zuwa Lafia domin yin zanga-zanga kan tallafin uwar gidan Shugaba Bola Tinubu
  • Masu zanga zangar sun yi zargin cewa gwamnatin jihar ta yi biris da su alhalin Sanata Remi Tinubu ta ba su gudunmawar N1bn
  • Sai dai, hukumar SEMA ta jihar Benue ta ce an ba da tallafin ne don a gyara matsugunnin 'yan gudun hijirar ba don a raba masu ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a Benue sun fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Laraba, inda suka mamaye babban titin Makurdi zuwa Lafia.

'Yan gudun hijirar dai sun mamaye titin ne domin yin zanga-zanga kan gudummawar da uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta bayar.

'Yan gudun hijira sun zargi gwamnatin Benue da kin ba su tallafin N1bn da matar Tinubu ta ba su
'Yan gudun hijira na zanga zanga a Benue bayan matar Tinubu ta ba su tallafin N1bn. Hoto: @HyacinthAlia
Source: Twitter

'Yan gudun hijira sun barke da zanga zanga

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

The Guardian ta rahoto cewa 'yan gudun hijirar sun yi ayari ayari kan hanyar, lamarin da ya kawo tsaikon zirga-zirgar ababen hawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata daga cikin masu zanga-zangar da ta bayyana sunanta da Dooshima ta ce an bar su cikin halin kuncin rayuwa ba tare da kulawa daga gwamnatin jihar ba.

Dooshima ta kara da cewa sun san kungiyoyi da mutane da dama sun kawo tallafin kudi, amma babu wani yunkurin a zo a gani na bunkasa rayuwarsu da gwamnati ta yi.

'Yar gudun hijirar ta ce:

"Jiya (Talata) uwargidar shugaban kasa ta zo nan ta ce ta ba da gudummawar Naira biliyan daya, amma har yanzu ba mu ji komai game da tallafin ba.
“Mutane da yawa suna zuwa suna bayar da gudummawa, amma babu wani taimakon kirki da gwamnatin jiha ke kawo mana.”

Benue: Hukumar SEMA ta yi martani

Da yake mayar da martani, jami’in yada labarai na hukumar agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Tema Ager, ya bayyana zanga-zangar a matsayin siyasa kawai, yana mai cewa gwamnati na kan tallafawa 'yan gudun hijirar.

Kara karanta wannan

Amurka ta gargadi gwamnonin Najeriya kan rashin kula da talakawa

A cewar Tema Ager:

“Wannan zanga-zangar ta barke ne bayan ziyarar da uwargidar shugaban kasa ta kawo jiya, inda ta sanar da bayar da gudummawar Naira biliyan daya.
“Ka sani, sau da yawa ana sanar da ba da tallafin kudade ne kawai, ba nan take ake bayar da su ba, dole sai an koma daga baya ake bayarwa.
"Don ta sanar da ba da tallafin kudin jiya ba shi ke nufin za a raba kudi a yau ba. Kuma abin lura a nan shi ne, kudin ba na abinci ba ne, na gyara masu matsugunni ne.
Gwamnatin Benue ta ce tallafin N1bn da matar Tinubu ta bayar ba na rabawa 'yan gudun hijira ba ne.
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba 'yan gudun hijira tallafin N1bn a Benue. Hoto: @HyacinthAlia
Source: Twitter

'Siyasa ce ta jawo zanga-zangar' - SEMA

Jaridar Punch ta rahoto Tema Ager ya ce akwai lokacin da 'yan gudun hijirar suka rika korafin cewa an ba da tallafin kudi a ba su, amma gwamnati ta ki raba masu, inda ya ce:

"Sau tari ana bayar da tallafin kudi ba wai don a raba masu kai tsaye ba, ana amfani da kudin ne don biya masu wasu bukatu.

Kara karanta wannan

Ana zaman ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Tinubu a Kaduna

“Zanga-zangar da suka yi siyasa ce ta haddasa ta. An shirya raba musu abinci tun makon jiya, amma wasu abubuwa suka kawo tsaiko. Yanzu kuma ana kan raba masu.”

Kokarin jin ta bakin jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Benue, DSP Udeme Edet, ya ci tura domin ba ta daga kiran waya ba.

An 'kunyata' matar Tinubu a Rivers

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu mata sun fice daga wajen taron tallafa musu da aka yi karkashin Sanata Remi Tinubu a jihar Rivers cikin fushi.

Matan sun fice ne don nuna bacin ransu kan yadda aka kyale matar Gwamna Siminalayi Fubara. aka ba matar kantoma abin magana a wajen taron.

Sai dai, duk da zanga-zangar da matan suka yi, taron ya ci gaba da gudana ba tare da cikas ba, inda matar kantomar, Theresa Ibas ta wakilci Sanata Oluremi Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com