Mutuwa Ta Girgiza Hukumar Zaɓe, Shugaban BASIEC Ya Rasu a Abuja

Mutuwa Ta Girgiza Hukumar Zaɓe, Shugaban BASIEC Ya Rasu a Abuja

  • Allah ya yiwa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama Hardawa rasuwa a Abuja
  • Ahmed Makama ya rasu ne ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a babban birnin tarayya Abuja
  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi alhinin wannan rashi, inda ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalansa da sauran ƴan uwa da abokan arziki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama Hardawa, ya riga mu gidan gaskiya.

Ahmed Makama, tsohon kwamishinan zaben INEC a jihohin Taraba da Nasarawa, ya rasu ne a ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, a birnin Abuja bayan gajerar rashin lafiya.

Shugaban hukumar zaɓen jihar Bauchi, Ahmed Makama Hardawa.
Allah ya karɓi ran shugaban hukumar BASIEC, Alhaji Ahmed Makama Hardawa Hoto: Abdullahi Abdu Babale
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana alhini da jimami matuka bisa wannan rashi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Iyalan Buhari sun bar gidan da aka birne tsohon shugaban ƙasa a Daura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Rasuwar shugaban BASIEC ta taɓa Najeriya'

Sanata Bala Mohammed ya ce rasuwar Ahmed Hardawa babban rashi ne ga jihar Bauchi da kasa baki daya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Laraba.

“A madadin ni kaina da iyalina, gwamnatin jiha da al’ummar Bauchi, ina mika ta’aziyya bisa rasuwar Alhaji Ahmed Makama Hardawa.”

Gwamna Bala ya faɗi halayen marigayin

Gwamna Bala ya bayyana marigayin a matsayin dattijo, kwararren jami’in gwamnati, kuma mai kishin kasa wanda ya bar tarihi mai inganci ta hanyar hidima ga Bauchi da Najeriya baki daya.

“Ya kasance tsohon Kwamishinan Zabe na INEC a jihohin Taraba da Nasarawa, inda ya gudanar da ayyukansa da gaskiya, jajircewa, da adalci, wannan ne dabi’un da aka sanshi da su a tsawon aikinsa.
“A matsayinsa na Shugaban BASIEC, Alhaji Ahmed Makama Hardawa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin dimokuradiyya a matakin ƙananan hukumomi ta hanyar shirya zaɓe mai sahihanci da gaskiya.”

Kara karanta wannan

Sarkin Gusau da wasu manyan sarakuna da suka rasu cikin wata 1 a Najeriya

- Gwamna Bala Mohammed.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala.Muhammed ya yi alhinin rasuwar shugaban hukumar zaɓe Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Gwamnatin Bauchi ya miƙa sakon ta'aziyya

Ya ƙara da cewa marigayin mutum mai mai hikima, tawali’u, da nagarta a fagen shugabanci, sannan ya ba da gudummuwa matuƙa wajen ci gaban dimukuraɗiyya, in ji rahoton Punch.

Gwamna Bala ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin, jami’an BASIEC, abokai da hadiman marigayin, da kuma al’ummar Hardawa da Masarautar Misau.

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa, Ya yaƙwata kabarinsa, Ya saka masa da Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa da abokansa hakurin jure wannan babban rashi.

Hakimin Hanafari ya rasu a Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa Iyan Jama'are kum Hakimin Hanafari, Alhaji Ahmed Nuhu Wabi ya rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Bauchi.

Bala Mohammed ya bayyana marigayi Ahmed Nuhu Wabi a matsayin basarake mai ƙima kuma ɗa ga mai martaba Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Wabi.

A madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi, Bala ya miƙa ta’aziyyarsa ga masarautar Jama’are, iyalan marigayin da kuma dukan waɗanda lamarin ya shafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262