Nuhu Ribadu Ya Fadi Nasarorin da Aka a Samu a Gwamnatin Tinubu kan Samar da Tsaro
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya nuna gamsuwarsa kan nasarorin da aka samu a fannin tsaro
- Nuhu Ribadu ya bayyana cewa hare-haren 'yan bindiga da Boko Haram sun ragu sosai a cikin shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu
- Ya nuna cewa an samu wadannan nasarorin ne sakamakon umarnin da shugaban kasa ya ba hukumomin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi magana kan hare-haren Boko Haram da 'yan bindiga a gwamnatin Mai girma Bola Tinubu.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram, ta'addancin 'yan bindiga da rikice-rikicen kabilanci a Arewacin Najeriya sun ragu sosai a cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne yayin wani taro na kwanaki biyu da gidauniyar Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Ribadu ya ce kan rashin tsaro?
Mai ba shugaban kasan shawara kan harkokin tsaron ya ce hare-haren sun ragu ne idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a gwamnatin da ta gabata.
A cikin misalan da ya bayar, Nuhu Ribadu ya ce mutane 1,192 ne suka mutu, fiye da 3,348 kuma aka sace a jihar Kaduna a zamanin gwamnatin da ta gabata.
Haka kuma, mutane sama da 5,000 sun rasa rayukansu a jihar Benue a cikin wannan lokacin.
Meyasa tsaro ya inganta karkashin Tinubu?
Ribadu ya ce nasarorin da aka samu a yaki da rashin tsaro sun biyo bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumomin tsaro na yin aiki tare da tsari guda wajen samar da tsaro.

Source: Facebook
Ya ce ayyukan tsaro da ake gudanarwa a shiyyoyin Arewa maso Yamma sun kai ga kubutar da mutane 11,259 da aka sace har zuwa watan Mayu na shekarar 2025.
Haka kuma, ya bayyana cewa an kashe wasu fitattun shugabannin 'yan bindiga da mambobin kungiyoyinsu a jihohin Zamfara, Kaduna da Katsina ta hannun jami’an tsaro.
Mai ba da shawarar kan harkokin tsaron ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani na Kaduna bisa ɗaukar salon warware rikice-rikice ta hanyar ba da dama ga hanyoyin sulhu da zaman lafiya, musamman a yankin Kudancin Kaduna, Birnin Gwari da sauran wuraren da ke fama da rikici a jihar.
Karanta wasu labaran kan Nuhu Ribadu
- Tsaro: Nuhu Ribadu ya ba Tinubu kariya, ya gargadi 'yan adawan Najeriya
- Nuhu Ribadu ya koka kan rashin tsaro, ya fadi adadin 'yan Najeriya da matsalar ta shafa
- APC ta tsage gaskiya kan batun goyon bayan Ribadu ya maye gurbin Shettima
Ribadu ya yabi Shugaba Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nuhu Ribadu ya yabi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yadda ya ceto Najeriya.
Mai ba shugaban kasan shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa bayan hawansa kan madafun iko.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar tarin matsaloli da kalubale kafin hawan Tinubu mulki a shekarar 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
