"Ku Yi Hattara": EFCC Ta Bankado Sabuwar Hanyar da Ake Damfarar 'Yan Najeriya

"Ku Yi Hattara": EFCC Ta Bankado Sabuwar Hanyar da Ake Damfarar 'Yan Najeriya

  • EFCC ta gano wata sabuwar dabara da masu damfara ke amfani da ita ta hanyar tallar tikitin jirgi domin satar bayanan mutane
  • Masu damfarar na bukatar mutane su biya ₦500 a matsayin gudunmawar jinkai, sai su yi kutse su sace bayanan sirri kamar BVN
  • EFCC ta ce an gano ‘yan damfara kusan 12,000 da ke amfani da wannan dabara a fadin kasar, suna bude asusu, su yi safarar kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta bankado wata sabuwar hanya da wasu miyagu ke amfani da ita wajen safarar kudi da damfarar 'yan Najeriya.

EFCC ta ce 'yan damfarar sun zo da sabon salo na damfara, don haka ta ga ya dace ta ankarar da 'yan kasar don su kula da bayanan bankunansu.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa, sarakuna da manyan da ba su halarci jana'izar Buhari ba a Daura

Hukumar EFCC ta gano sabuwar hanyar da masu damfara ke amfanida ita wajen safarar kudade
Hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ke Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Sabuwar damfara da EFCC ta gano

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Juma'a, EFCC ta ce masu damfarar suna amfani da tallar tikitin jiragen sama a farashi mai rahusa don yaudarar mutane.

"Wannan damfarar ta shafi amfani da wata fasaha ta yin kutse ga bayanan da mutane suka shigar yayin sayen tikitin jiragen da suka tallata," a cewar sanarwar.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ce 'yan damfarar na amfani da kalamai masu jan hankali kamar, "Garabasa," "Dama ta samu," duk don jan ra'ayin mutane zuwa gare su.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Ana jan hankalin waɗanda za a damfarar su bayar da bayanan asusun ajiyarsu. Ta haka ne masu zambar ke aiwatar da mu'amalolin kudi a madadinsu ta hanyar tura kuɗaɗensu zuwa asusun ajiyar kuɗi galibi a bankunan intanet.
"Ta wannan damar ce kuma, masu zambar suke iya sarrafa asusun, su kuma wanke kuɗaɗen da suka tura ta hanyar sayen kuɗaɗen crypto."

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Kotu ta umarci ƴan sanda su biya masu zanga zanga diyyar N10m

Yadda sabuwar damfarar ke aiki

EFCC ta buga misali da wata garabasa da ke ba da rangwamen kashi 50 na kudin tikitin jirgi. An bukaci mutane su biya N500 ga asusun kamfanin jirgin, ta nan suke samun bayan mutane.

Hukumar ta ci gaba da cewa:

"Ana yaudarar waɗanda ake so a damfara da cewar za su samu garabasar ragin kaso 50 din ne kawai idan suka sauke manhajar kamfanin jirgin saman.
"Sai dai, bayan sun sauke manhajar da kuma sun shigar da bayanan su ba tare da wani zargi, sai a rika tura kuɗaɗe daga asusun bankin su zuwa wani asusu a bankunan intanet."
Hukumar EFCC ta ce akwai mutane akalla 12000 da suka shiga wannan sabuwar hanyar damfarar mutane
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta gano masu damfara 12,000

Hukumar EFCC ta ce wannan wata sabuwar hanyar damfara ce da wasu gungun 'yan Najeriya suka bullo da ita, inda har suke ba mutane kyautar N1,500 zuwa N2,000 don samun bayanansu.

EFCC ta ce su kuma suna sayar da bayanan da suka samu ga wasu kamfanonin hada-hadar kudi na intanet a kan N5,000.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu

"Bayanan da EFCC ta samu sun nuna cewa wadannan gungun madamfara sun tasamma 12,000 kuma suna a ko ina fadin kasar, inda suke karbar bayanan BVN, hoton fasfo da sauran bayanan mutum.
"Ana amfani da wadannan bayanan domin bude asusu da bankunan intanet, sai kuma ayi amfani da asusun wajen yin damfara da safarar kudi."

- Hukumar EFCC.

Yadda 'yan siyasa ke satar kudin jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC ta bankado manyan 'yan siyasa da ke amfani da 'yan 'Yahoo-Yahoo' wajen safarar biliyoyin kuɗin sata zuwa ƙasashen waje.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an gano yadda 'yan Yahoo ke bude asusun crypto tare da tura kuɗaɗen da 'yan siyasar ke ba su don sayen kadarori.

Mista Olukoyede ya kuma nuna damuwar cewa 'yan damfara sun koma fashi, garkuwa da mutane, da kisan kai don tsafi idan damfara ta gaza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com