Yobe: Wata Mata, Hadiza Mamuda Ta Kashe Mijinta kan Abin da Yake Kawo Mata Kullum

Yobe: Wata Mata, Hadiza Mamuda Ta Kashe Mijinta kan Abin da Yake Kawo Mata Kullum

  • Jami'an ƴan sanda sun damƙe wata mata, Hadiza Mamuda bisa zargin kashe maigidanta kan abinci a ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan a Damaturu ranar Laraba da ta shuɗe
  • Kwamishinan ƴan sanda ya nuna ɓacin ransa kan lamarin inda ya roƙi malamai su ƙara dagewa wajen faɗakar da al'ummar illar rikicin ma'aurata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Wata mata mai suna, Hadiza Mamuda, yar kimanin shekara 35 a duniya ta hallaka mijinta a ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta zama ajalin mijin ne sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsu har suka yi faɗa da doke-doke kan kayan abinci.

Mata ta kashe mijinta a Yobe.
Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da kisan mijinta a Yobe Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƴan sanda sun kama Hadiza Mamuda

Kara karanta wannan

Dakarun tsaro da mafarauta sun hada hannu, an yi fata fata da 'yan ta'adda

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe, reshen karamar hukumar Fika, ta cafke Hadiza Mamuda bisa zargin aikata laifin kisan kai, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan mummunan al'amari ya faru ne a ƙauyen Garin Abba da ke yankin ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ta Arewa maso Gabas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan ga ƴan jarida a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, a ranar Laraba.

Yadda matar ta narkawa mijinta itace

A cewarsa, ana zargin wacce ake tuhuma da amfani da wani itace wajen bugun mijinta har ya mutu.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya kara da cewa yanzu haka suna kan bincike don gano abin da ya faru tsakanin ma'auratan wanda ya kai ga kisan kai.

Ya kuma tabbatar wa al'umma musamman ƴan uwan mamacin cewa da zaran an gama bincike, rundunar ƴan sanda za ta gurfanar da matar a gaban kotu don ta girbi abin da ta shuka.

Bayanai sun nuna cewa mamacin, yana da mata biyu da yara biyar ciki har da wadanda matar da ake tuhuma, Hadiza Mamuda ta haifa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Sai dai a yanzu iyalansa da ƴan uwa da ma al'ummar garin na cikin ƙunci da takaicin abin da ya auku.

Yan sanda sun kama matar da ake zargi.
Kwamishinan ƴan sanda ya buƙaci malamai su dage wajen faɗakar da al'umma Hoto: Nigeria Police
Source: Getty Images

Kwamishinan ƴan sandan Yobe ya ja hankali

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gobe, CP Emmanuel Ado, ya jaddada bukatar hadin gwiwa daga al’umma wajen dakile matsalolin tashin hankali a cikin gida da cin zarafi.

Ya bukaci malaman addinai da su kara zage damtse wajen fadakar da jama’a kan hadurran tashin hankali tsakanin ma’aurata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da aiki tuƙuru ba dare ba rana wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Yobe.

Magidanci ya kashe matarsa a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa wani magidanci ɗan kimanin shekara 31, Mohammed Sani ya yi sanadiyyar ajalin matarsa mai suna Hauwa a jihar Neja.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya ce sun samu labarin aika-aikar da magidancin ya yi kuma tuni aka kama shi.

Wasu bayanai sun nuna cewa Hauwa na da juna biyu da ya kai watanni tara kafin wannan lamari mara daɗi ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262