Karshen Alewa: Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram da Mayaka Masu Yawa

Karshen Alewa: Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram da Mayaka Masu Yawa

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile harin Boko Haram a Monguno da Bitta, inda suka kashe kwamandan mayakan, Ibn Khalid
  • Dakarun sun kwato bindigogi, alburusai, bama-bamai da kyamarar daukar bidiyo yayin da suka bi sawun 'yan ta’addan da suka tsere
  • A wasu hare-haren daban a yankin Sambisa zuwa Kaga da Madagali, an kashe 'yan ta'adda 17 kuma an kwace babura da kayayyakinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram da suka kai hari a garuruwan Monguno da Bitta da ke jihar Borno.

A yayin artabun da suka yi, dakarun sojojin sun samu nasarar kashe mayaka da dama ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe babban kwamandan Boko Haram a Borno
Wasu daga cikin dakarun sojojin Najeriya da ke aiki a karkashin Operation Hadin Kai (OPHK). Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin ƙasa, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya sanar da cewa sojojin sun dakile yunkurin 'yan ta'addan na shiga Monguno, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji sun daƙile mugun shirin ƴan ta'adda, sun kashe mai ɗaukar bidiyo domin yaɗa ƙarya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyaftin Reuben Kovangiya:

“Dakarun sun ƙaddamar da luguden wuta mai ƙarfi yayin da ‘yan ta’addan ke ƙoƙarin kai harin, lamarin da ya haifar da kashe wasu daga cikinsu ciki har da babban kwamandan su Ibn Khalid da kuma mai daukar bidiyon su."

Ya ƙara da cewa, yayin da sojojin ke bin sawun 'yan ta’addan da suka gudu, sun gano alamun jini a hanyoyin da suka bi.

An kwato makaman 'yan ta'adda a Borno

Kayan da aka gano sun haɗa da: alburusai masu yawa na 7.62mm, bel ɗin PKT ɗaya, bindigar AK-47 guda ɗaya, bama-bamai na RPG da wasu kayayyaki daban-daban.

“Dakarun sun kuma kwato wasu bindigogi, makaman AK-47, da kyamarar daukar bidiyon ‘yan ta’addan, yayin da bincike ke ci gaba don hana su samun damar sake kai farmaki.”

- Kyaftin Reuben Kovangiya.

Channels ta rahoto Kyaftin Kovangiya ya na cewa sojoji sun kara kaimi sosai wajen ganin sun kakkabe 'yan ta'addan da ke addabar Borno da ma jihohin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga a Neja, an samu asarar rayuka

Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ta ce dakarunta sun dakile harin Boko Haram a Borno
CDSA Lanre Oluwatoyin (AVM) ya ziyarci hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai a Maiduri. Hoto: @NigeriaArmyInfo
Source: Twitter

Borno: Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda

A wasu hare-haren daban da aka kai a lokaci ɗaya, an kashe ‘yan ta’adda 17 a faɗin Sambisa har zuwa kananan hukumomin Madagali da Kaga, tare da kwace babura da sauran kayayyaki.

Sanarwar ta ce:

“Babban kwamandan rundunar ya yaba da ƙarfin hali da juriyar da sojojin suka nuna, ya kuma bukaci su ci gaba da nuna jajircewa a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda.”

A wani farmaki makamancin haka a Bitta, sojojin sun dakile wani yunkurin hari da ‘yan ta’adda suka yi, inda suka kashe wasu daga cikin su, ciki har da wani babban kwamanda.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile yunkurin harin ‘yan ta’adda a Neja, inda suka kashe wasu daga cikin maharan.

Bayan samun bayanan sirri, sojojin tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama suka kaddamar da farmaki cikin tsari, wanda ya haifar da nasarar kwato bindigogi da sauran makamai.

Sai dai duk da wannan nasara, soja guda ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar, inda rundunar ta sha alwashin ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a yankin Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com