Kano: Kotun Tarayya Ta Tunkuɗa Ƙeyar Ɗan TikTok, G Fresh Zuwa Gidan Kaso
- Shahararren dan TikTok daga Kano, Abubakar Ibrahim (G-Fresh) ya shiga matsala bayan kotu ta same shi da laifin cin zarafin Naira a jihar
- Kotun tarayya ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali ko ya biya tara N200,000 bayan ya amsa laifinsa ba tare da wani bata lokaci ba
- An zargi G-Fresh da cin mutuncin Naira a shagon yar TikTok mai suna Rahama Sa’idu da ke karamar hukumar Tarauni da ke birnin Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shahararren dan TikTok a jihar Kano, Abubakar Ibrahim ya sake burmawa matsala bayan karya dokoki musamman da suka shafi takardun Naira.
Matashin dan TikTok da aka fi sani da G-Fresh ya shiga matsala ne bayan hukuncin da kotu ta yanke a kansa.

Source: Facebook
Rahoton Leadership Hausa ya tabbatar da cewa kotun tarayya da ke Kano ta tasa keyar G-Fresh zuwa gidan kaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalolin da G-Fresh ya jawowa kansa a baya
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake maka G-Fresh a gaban kotu kan wasu abubuwa da yake yi musamman a kafofin sadarwa ta zamani na Facebook da TikTok.
Matashin ya sha jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa wanda wasu ke ganin abin da yake yi ya saba ka'ida da al'adar Bahaushe da kuma tsarin Musulunci.
Abin da ya faru tsakanin G-Fresh, Sadiya Haruna
Bayan cafke shi da Hisbah a kwanaki baya, tsohuwar matarsa ma ta taba maka shi a gaban kotu tun a watan Satumbar 2023.
Tsohuwar jarumar ta Kannywood, Sadiya Haruna ta kai G-Fresh a gaban kotu tana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu da matashin.
G-Fresh ya tubure yana son matarsa inda alƙalin kotun ya ƙara musu lokaci domin su je su sasanta tsakaninsu.

Source: TikTok
Kano: Musabbabin daure G-Fresh a gidan kaso

Kara karanta wannan
Janar Tukur Buratai ya tsage gaskiya, ya fadi abin da ke shigar da matasa ta'addanci
Majiyoyi sun tabbatar da cewa kotun ta dauki matakin ne bayan samun matashin da cin zarafin Naira, cewar Aminiya.
Bayan karanto masa dukan abin da ake zarginsa da su, G-Fresh ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa a kansu.
Kotun daga bisani ta yanke masa hukuncin daurin wata biyar a gidan gyaran hali ko zabin biyan tarar N200,000.
Ana zargin G-Fresh ne da cin mutuncin Naira a shagon wata yar TikTk da ake kira Rahama Sa'idu da ke Tarauni.
Hukumar Hisbah ta kama G-Fresh a Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar Hisbah ta Kano ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen.
An ce hukumar ta kama mawakin ne bayan tarin gargadi da ta yi masa kan kalamai, rawa da bidoyon batsa da ya ke yadawa a TikTok da kuma manhajar Facebook.
Haka zalika, a wancan lokaci an zargi G-Fresh Al'ameen da yin izgili ga ayoyin Al-Kur'ani, wanda aka shirya gurfanar da shi gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
