Janar Tukur Buratai Ya Tsage Gaskiya, Ya Fadi Abin da Ke Shigar da Matasa Ta’addanci

Janar Tukur Buratai Ya Tsage Gaskiya, Ya Fadi Abin da Ke Shigar da Matasa Ta’addanci

  • Tsohon hafsan sojojin kasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya yi magana kan abubuwan da ke kara ta'addanci a Arewacin Najeriya
  • Buratai ya jaddada cewa rashin gwamnati a yankunan da ba a kula da su na taimakawa wajen daukar matasa cikin kungiyar ta’addanci
  • Ya ce tilas ne a karfafa matasa domin su zama ginshikan ci gaba, ba barazana ba ga zaman lafiya da makomar Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Tsohon shugaban hafsoshin sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya yi magana kan matsalolin ta'addanci.

Tukur Buratai ya bayyana dalilan da ke haddasa shigar matasa kungiyar Boko Haram da ISWAP a Arewacin Najeriya.

Buratai ya kawo hanyar dakile matsalar tsaro
Tukur Buratai ya fadi dalilin matasa na shiga kungiyoyin ta'addanci. Hoto: HQ Nigeria Army.
Source: Twitter

Buratai ya fadi dalilin karuwar matasa a ta'addanci

Tsohon hafsan sojoji ya yi wannan bayani ne a yayin jawabinsa a wani taron karawa juna sani karo na 18 da Jami’ar Tarayya ta Lokoja ta shirya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi

Buratai ya bayyana cewa talauci da ware matasa daga al’umma na daga cikin manyan dalilan da ke jawo matasa shiga kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

A cewarsa, matsalar rashin wakilcin gwamnati a yankunan da ke nesa da birane na kara saurin yada akidar ta’addanci tsakanin matasa.

Ya ce idan ba a dauki matakai ba, matasa za su ci gaba da fada cikin hannun kungiyoyin da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban kasa.

Buratai ya ce Najeriya na da matasa fiye da kashi 60 cikin 100 na yawan jama’a, don haka dole ne a maida hankali wajen tallafa musu.

Ya ce:

"Matasa su ne ginshikan gina kasa idan aka horar da su da kyau, shugabanci nagari ne kadai zai dakile ta’addanci."
Buratai ya jawo hankalin hukumomi kan ta'addanci
Tukur Buratai ya fadi abin da ke sanya matasa cikin ta'addanci. Hoto: HQ Nigeria Army.
Source: Facebook

'Yadda za a magance matsalolin tsaro' - Buratai

Tukur Buratai ya jaddada cewa matsalolin tsaro ba za su magance kansu ba sai an hada su da gyare-gyaren tsarin shugabanci da karin kulawa ga matasa.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Buratai ya bayyana cewa idan ba a ba matasa dama ba, za su fada hannun miyagu ko makiya kasa, su zama barazana maimakon mafita, cewar Vanguard.

A cewarsa:

"Idan muka karfafa matasa, ba za su tsaya nan ba, za su kare kasar nan kuma su tsara makomarta da hankali da kishin kasa."

Ya ce matasa na da rawar gani a fannoni da dama kamar noma, fasaha, tsaro da kasuwanci idan aka ba su horo da damarmaki na ci gaba.

Buratai ya bukaci gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu su hada hannu wajen fadakarwa da horar da matasa a fadin Najeriya.

Buratai ya bukaci kawo karshen ta'addanci

Mun ba ku labari a baya cewa tsohon shugaban rundunar sojojin kasa, Tukur Buratai ya yi magana kan tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Buratai ya bukaci magance matsalolin tsaron yankin kafin lamarin ya kai ga yadda za a gaza magance sa.

Laftanal Janar Tukur Buratai mai ritaya ya yi jawabin ne a yayin wani taro da jami'ar Maiduguri ta shirya a ranar Litinin, 27 ga watan Mayun 2024.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.