Yada bikin dan Buratai kai tsaye a shafin yanar gizon rundunar gizo ya haifar da cece-kuce

Yada bikin dan Buratai kai tsaye a shafin yanar gizon rundunar gizo ya haifar da cece-kuce

- Rundunar soji ta sha caccaka sakamakon yada taron bikin Hamisu Tukur, dan Janar Yusuf Buratai

- Kwararru a harkar tsaro sun ce ko kadan yin hakan bai dace ba kuma ya kamata rundunar soji ta yi bayanin dalilin aikata hakan

- Wani masani ya bayyana cewa babu mamaki don rundunar soji ta yi hakan saboda shugaban kasa ma ya taba bawa diyarsa jirginsa na ofis don sha'anin kashin kanta

Ƙwararrun masana harkar tsaro sun magantu kan watsa bikin ɗan gidan Burutai kaitsaye a shafin sada zumunta na Facebook a shafin hukumar Rundunar soji ta ƙasa, kamar yadda HumAngle ta wallafa.

Rundunar sojin Najeriya ta watsa bikin ɗaurin auren Hamisu Tukur, ɗa ga shugaban Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, wanda aka yi a wani babban masallaci a unguwar Maitama da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Sai dai, ba'a ƙirkiri shafin hukuma musamman irin na rundunar soji don irin wannan ayyukan ba, musamman wanda suka shafi rayuwar cikin gidan shugaban sojoji da iyalansa ba.

An kasa gane dalilin da yasa Rundunar soji ta yi amfani da shafinta na sadarwa a hukumance don yaɗa al'amuran iyalan shugaban sojoji wanda ya kamata ace ya maida hankalinsa wajen gudanar da yaƙi da ta'addanci da ake fama da shi a sassa daban daban na ƙasar.

KARANTA: PANDEF: Muna son jin amsoshin tambayoyinmu uku daga bakin Buhari

Yada bikin dan Buratai kai tsaye a shafin yanar gizon rundunar gizo ya haifar da cece-kuce
Yada bikin dan Buratai kai tsaye a shafin yanar gizon rundunar gizo ya haifar da cece-kuce @HumAngle
Asali: Twitter

"An yi shafukan sadarwar hukumar rundunar soji ne don yaɗa bayanai, to hakan na nufin duk wani bayanin hukuma da rundunar ta ke son sanar da jama'a, ba wai irin wannan ba," acewar ƙwararren masanin tsaro, Kabiru Adamu.

Adamu ya ce kansa ya kulle akan yadda aka yi bikin kuma ya zama nauyin yaɗawar shafin sadarwar zamani na hukumar rundunar soji maimakon amfani da wasu kafafen wajen yaɗa shi.

KARANTA: FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu

"Abin bai yi dai-dai ba, kuma ina shawartar hedikwatar sojoji su bada bayanin dalilin aikata abu irin haka," a cewar Adamu.

Ya kara da cewa, "akwai abubuwa da dama da yakamata ace shafin ya haskawa jama'a musamman akan atisaye daban-daban da ake gudanarwa a yankunan ƙasar nan."

Confidence Isaiah-MacHarry, ƙwararren mai hasashen tsaro ya ce "ba tare da wata rufa rufa,wannan ya biyo bayan yadda shugaban ƙasa ya baiwa ƴar'sa jirginsa na ofis don yin al'amuran ƙashin kanta."

A ranar Juma'a ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria.

Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofshinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria

Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron Nigeria da aikatawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng