Najeriya Ta Ƙara Rasa Basarake, Wakilin Sardaunan Bauchi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Ƙara Rasa Basarake, Wakilin Sardaunan Bauchi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Wakilin Sardaunan Bauchi, Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar Abubakar Jafaru a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2025
  • Bala Mohammed ya yi alhinin wannan rashin tare da addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kuma ya ba iyalansa haƙuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Hadimin gwamnan jihar Bauchi kuma mai riƙe da sarautar Wakilin Sardaunan Bauchi, Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah ya riga mu gidan gaskiya.

Gwamnatin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ne ta sanar da rasuwar Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah.

Wakilin Sardaunan Bauchi, Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah.
Wakilin Sardaunan Bauchi, Jafaru Ilelah ya riga mu gidan gaskiya Hoto: @mahbeel_A
Source: Twitter

Wakilin Sardaunan Bauchi ya rasu

Rahoton Leadership ya nuna cewa Alhaji Jafaru Ilelah ya rasu ne a ranar Talata bayan gajerar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Buhari: Majalisar dattawa ta shirya karrama tsohon shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsa, an nada Alhaji Jafaru Ilelah kwanan nan a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Jama'a ga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.

Marigayi Abubakar Jafaru gogaggen manomi ne kuma ƙwararren masani a harkar ci gaban noma, wanda ya bayar da gudummawa wajen bunƙasa noma a Jihar Bauchi.

Ya taɓa rike mukamin Manajan Shirin Ci Gaban Noman Jihar Bauchi (BSADP), wanda ya sauka bayan shekaru masu yawa na yi wa al'umma hidima.

Gwamna Bala ya yi alhinin rasuwar hadiminsa

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana mamacin a matsayin gwarzon ɗan jarida, kuma gogaggen ɗan siyasa mai ƙwarin gwiwa wajen jawo jama'a daga tushe.

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar jiya Talata.

Bala ya ce marigayin jajirtaccen ma’aikacin gwamnati ne da za a dade ana tunawa da gudummawarsa a fannin wayar da kan al'umma da haɗin kai.

Kara karanta wannan

2027: Sarkin Daura ya fadi wanda masarautar za ta zaba a gaban matar Tinubu

Gwamna Mohammed, a sakon ta’aziyyarsa a madadin iyalansa, gwamnatin jihar da al’ummar Jihar Bauchi, ya bayyana rasuwar Abubakar Jafaru da babban rashi.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya yi ta'aziyyar rasuwar Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Gwamnan Bauchi ya yi wa marigayin addu'a

Ya ƙara da cewa marigayin ɗan ƙasa ne nagari, mutumin kirki mai daraja, kuma ginshiƙin haɗin kai, wanda za a yi kewar hikimarsa da hidimar da yake yi wa al'umma.

Gwamnan ya yi addu’ar samun rahamar Allah ga marigayin, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya sa shi a gidan Aljannah.

Ya kuma.roki Allah Ya ba iyalansa, dangi, Majalisar Masarautar Bauchi, kafafen yaɗa labarai, da daukacin jama’ar Jihar Bauchi haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

Iyan Jama'are ya rasu a jihar Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa Iyan Jama'are kuma Hakimin Hanafari, Alhaji Ahmed Nuhu Wabi ya rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana jimami da alhini kan rasuwar Alhaji Ahmed Nuhu Wabi, Iyan Jama’are, yana mai cewa an yi babban rashi.

Gwamna Bala, a madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi, ya miƙa ta’aziyyarsa ga masarautar Jama’are, iyalan marigayin da kuma dukan waɗanda lamarin ya shafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262